An Kashe Yan Bindiga Yayin da Suka Yi Yunkurin Kai Hari a Arewa
- Jami'an tsaro sun bindige wasu tsagerun yan bindiga yayin da suke dakile wani hari da suka yi yunkurin kaiwa kauyen Tse Gaagum a jihar Benue
- An rahoto cewa jami'an tsaron sun yi zazzafan arangama da yan bindigan bayan sun samu kira daga wajen mutanen kauyen
- Yan bindigar sun farmaki garuruwan da ke kusa da kauyen tun da sanyin safiya inda su kuma suka gaggauta kiran jami'an tsaro wadanda suka amsa kira cikin gaggawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Jihar Benue - Jami'an tsaro a safiyar Laraba, 17 ga watan Janairu, sun hallaka wasu yan bindiga, yayin da suke kokarin dakile harin da suka yi yunkurin kaiwa al'ummar kauyen Tse Gaagum.
An dai yi musayar wuta mai zafi tsakanin jami'an tsaron da yan bindigar a kauyen Tse Gaagum dake gudunmar Ukemberegya, a karamar hukumar Logo dake jihar Benue, rahoton Daily Trust.
Wasu da abun ya faru a idonsu sun shaidawa manema labarai cewa, jami'an tsaron sun fatattaki yan bindigar bayan fakar su da suka yi sakamakon kiran gaggawa da suka samu daga mazauna kauyen.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mazauna kauyen sun ce yan bindigar sun yiwa mutanen garin kawanya ne tun wajen misalin ƙarfe 4:00 na Asubah, kuma ba tare da bata lokaci ba suka sanar da jami'an tsaro a sirrance.
Daya daga cikin yan kauyen da ya bukaci a sakaya sunan sa ne ya shaidawa manema labarai wannan ci gaba da suka samu.
Wani mazaunin kauyen da ya nemi a sakaya sunansa ya ce:
"Tun wajen karfe 4:00 na Asubah suka katange mu, kuma abin ban sha'awa shi ne yadda jami'an tsaro suka kawo mana dauki cikin gaggawa."
Martanin mahukunta kan harin da aka dakile
Da aka tuntubi mai bai wa gwamnan jihar shawara kan harkokin tsaro, da harkokin cikin gida Cif Joseph Har, ya godewa mazauna kauyen kan saurin sanar da su da suka yi, kuma a cewarsa hakan ya taimaka musu.
Har ya ce:
"Na samu labarin cewa jami'an tsaro a Logo sun samu kira mai cike da damuwa daga mazauna kauyen Tse Gaagum, a safiyar yau (Laravba) sun harbe biyu daga cikin yan bindigar da suka farmaki garin.
"Sun yi nasarar samo babur kirar Bajaj mallakin daya daga cikin mutanen kauyen. Sauran kayayyakin sun hada da bindiga kirar AK47 da harsasai shida, adda, layu iri-iri."
Har kawo lokacin haɗa wannan rahoto ba a samu ji daga bakin mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Benue Catherine Anene ba, kuma bata amsa kiran wayar da aka mata ba, rahoton Trust Radio.
Yan bindiga sun bukaci babura da abinci
A wani labarin, mun ji cewa masu garkuwa da mutanen da suka sace mutum 23 a kauyen Kawu, yankin Bwari a babban birnin tarayya Abuja, sun tisa keyar wadanda suka sace zuwa wani jeji a garin Akilbu.
Bayan komawa da mutanen garin Akilbu da ke hanyar titin Kaduna zuwa Abuja, maharan sun kuma bukaci yan uwansu da su kawo masu babura biyar da kayan abinci.
Asali: Legit.ng