Kano: Doka Ta Haramta Yin Lefe Da Kayan Daki, Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani
- Wani lauya mai suna Abba Hikima ya ce doka ta hana yin lefe, kayan daki, kayan na gani ina so da sauran tsarabe-tsaraben aure a jihar Kano
- Barista Hikima ya ce dokar ta tanadi hukuncin dauri da tara ko kuma kotu ta haɗawa mutum duka biyun
- A cewar lauyan, tun a zamanin mulkin soja ne aka samar da dokar a Kano, kuma har yanzu tana aiki ba tare da wata doka ta danne ta ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fanni n nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Kano - A yayin da masu shirin yin aure ke kuka kan tilascin yin lefe a wannan tsadajjen lokaci, musamman ma matasa, wani lauya ya ce akwai dokar da ta hana yin lefe a jihar Kano.
Barista Abba Hikima ya ce akwai wata tsohuwar doka da aka samar tun zamanin mulkin sojoji, wacce ta haramta duk wasu tsarabe-tsarabe na aure da ba addini ne ya kawo su ba.
Me doka ta ce game da dokokin da aka yi a mulkin soja?
A tattaunawarsa da kafar yaɗa labarai ta DW Hausa, Barista Hikima ya ce dokar ta haramta kayan lefe, kayan na gani ina so, kuma har ta tanadi hukunci akan duk wanda ya aikata su.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
La'akari da cewa an samar da dokar tun a zamanin mulkin soja, lauyan ya ce:
"Sashe na 315 na mulkin Najeriya ya fadi cewa duk da an dawo da dimokuraɗiyya, za a ci gaba da amfani da dokokin da aka yi a mulkin soja da ba su saba wa tsarin mulkin Najeriya ba."
Hukuncin da dokar hana lefe ta tanada a jihar Kano
Barista Hikima ya ce dokar ta ba 'yan sanda damar kama duk wanda ya je ya yi lefe mai yawa da ya wuce hankali, kuma wanda ya karba ma yana da laifi.
Ya ce idan har aka samu wanda zai yi aure ya yi lefe ko iyaye suka karbi lefen, to kotu iya yanke masu hukunci kamar:
"Daurin gidan yari na wani lokaci, ko biyan tara, ko kuma kotu ta haɗa wa mutum duka biyun watakan biyan tarar da kuma zaman gidan kaso.
"Idan har aka samu hadin kai tsakanin wanda ya yi lefe, da wanda ya karbi lefen, da wanda ya ba da goyon baya aka yi lefen, to duka 'yan sanda za su iya kama su bisa sahalewar doka."
Dokar ba za ta yi tasiri ba - Abba Gezawa
Wani da Legit Hausa ta zanta da shi, Abba Hassan Gezawa, ya ce zakulo wannan dokar da lauyan ya yi abu ne mai kyau, amma kamar ihu ne bayan hari.
Gezawa ya ce ana cikin wani zamani wanda yin kayan lefe, kayan daki ya zama kamar wajibi ne a hidimar aure, gaza yin su na iya kawo nakasu ga dorewar auren.
Ya ce:
"Wannan doka muna maraba da ita, amma ina tabbatar maka babu wani tasiri da za ta yi a Kano. Kana ganin yadda maza da mata ke kukutawa su yi aure, yanzu ace ba lefe da sadaki?
"Namiji na iya nemo gida, amma shi zai yi kayan daki da kayan kitchen? Ita matar da shigo da kayan jikinta kawai? Ai daga ji kai kasan ba lallai auren ya dore ba, kuma za a samu yawaitar sakin aure."
Abba Gazawa ya ce abin da ya fi dacewa shi ne a samar da dokar da za ta kayyade kayayyakin lefe da na daki, hakan zai fi amma ba wai a haramta yin su ba.
Kotu ta fara yanke hukunci kan shari'ar BBC da mawakin Kano
A wani labarin kuma, wata kotun tarayya da ke Kano ta fara yanke hukunci kan shari'ar da sa ke yi tsakanin wani Jamal Abdul da ya shigar da BBC kara.
Mawaki Kamal ya shigar da kafar yaɗa labaran kara ne saboda ta yi amfani da sautin wakarsa a shirinta na 'Daga bakin mai ita' ba tare da izininsa ba.
Asali: Legit.ng