Majalisar Shari'a Musulunci Ta Yi Nadamar Goyon Bayan 'Muslim-Muslim Tiket' Ta Gwamnatin Tinubu
- Majalisar koli ta shari'ar Musulunci ta kasa ta koka da salon mulkin gwamnatin Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu
- Majalisar SCSN wacce ta ce ta dawo daga rakiyar gwamnatin Tinubu, ta ce ya yi watsi da muradin Musulmi bayan sun sha wahalar zabensa a 2023
- Magatakardar Majalisar, Baba Ahmed ya ce kungiyoyi da malamai suna ganin an kai su an baro tun da aka sa su yin tikitin Musulmi da Musulmi wanda a yanzu bai kare su da komai ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Abuja - Majalisar shari'ar Musulunci ta kasa (SCSN) ta bayyana matsayinta a kan goyon bayan gwamnatin Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.
A cewar ta, ta dawo daga rakiyar gwamnatin ta APC bayan ta zargi Tinubu da yin watsi da muradin Musulmi a kasar.
Majalisar ta bayyana haka ne a yayin wani taro da ta kira na kwanaki biyu, a babban birnin tarayya Abuja domin nazari kan abubuwan da suka biyo bayan babban zaben kasar na 2023.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me yasa majalisar Musulunci ta dawo daga rakiyar gwamnatin Tinubu?
A hirarsa da sashin Hausa na BBC, magatakardar majalisar ta Musulunci, Nafiu Baba Ahmed, ya bayyana cewa sun kira taron ne domin sauraron koke-koken mutane kan abubuwan da suka biyo bayan zaben.
Baba Ahmed ya ce:
"Mu muka shige gaba wajen tattara kungiyoyin Musulmai da malamai domin su mara wa tikitin da ya kai wannan gwamnati ga nasara a zaben.
"Sai ga shi yanzu malamai da kungiyoyin addini suna fitowa suna cewa an kai su an baro, an yi tikitin Musulmi da Musulmi amma an yi watsi da muradin Musulmai wadanda suka sha wahala wajen zaben gwamnatin."
Har wayau, ya bayyana cewa taron wata dama ce da dukkanin kungiyoyi da jama'a za su iya zuwa don bayyana matsalolin da suka addabe su a kan wannan gwamnati, kasancewar ba a cik masu alkawaran da aka daukar ma su ba.
Magatakardar kuma ce majalisar ta yi danasanin rawar ganin da ta taka soboda a cewarsa; 'Mun tura mota ta tashi ta bade mu da kura da hayaki, ta tafi ta bar mu a tsaye.'
Ya kuma ce dole ne a sake zurfafa tunani kafin a yanke hukunci idan har dama irin wannan ta sake samuwa a nan gaba, rahoton BBC Hausa.
Majalisar Musulunci bata sayar da mutuncinta ba, Baba Ahmed
Sai dai kuma, Baba Ahmed ya yi watsi da ikirarin cewa majalisar ta sayar da mutuncinta, yana mai cewa a kullun suna kokari wajen ganin sun janyo hankalin gwamnati idan har ta kuskure.
Ya kuma ce hatta shi kansa shugaban kasar sai da suka kalle shi cikin ido suka sanar da shi cewa bai kyauta ba, saboda rashin cika alkawaran da ya daukarwa mutane.
Legit Hausa ta zanta da wani dan Najeriya, Muhammad Sani wanda ya yi Tinubu da Shettima saboda kasancewarsu Musulmi.
Mallam Sani ya ce:
"Lallai mun tafka babban kuskure da ba zai gogu ba kuma muna ji a jikinmu. Mun bi tsarin addini a lokacin zaben don a tunaninmu bai kamata mu bar na gida mu je dawa ba.
"Ko a wajen rabon mukamai an fi ba kiristoci yan kudu fifiko sama da mu yan arewa wadanda mune muka zabi gwamnatin Tinubu.
"Ya kamata shugaban kasar nan ya duba Allah ya kawo mana sassauci a halin da muke ciki. Amana ne muka basa kuma idan ya ci mana Allah ba zai barsa ba.
"Haka suma shugabannin Musulunci suna da nasu domin sune suka dunga tallata wannan tikiti sai ga shi an bar mu a ciki. Allah dai ya kyauta, ya kuma dubi niyarmu ta alkhairi ya kawo mana mafita a wannan kangi da muke ciki."
Sunday Igboho ya magantu kan mulkin Tinubu
A wani labarin, mun ji cewa mai fafutukar kasar Yarbawa, Sunday Adeyemo, wanda aka fi sani da Sunday Igboho, ya jinjinawa Shugaban kasa Bola Tinubu kan daukar matakan da suka dace don farfado da Najeriya.
Igboho ya ce Shugaban kasar na yin abubuwan da suka kamata da daukar matakan da suka dace a wata hira da gidan talbijin na Alaroye ta yanar gizo a karshen mako.
Asali: Legit.ng