N585m: EFCC Ta Titsiye Akanta Janar a kan Zargin Badakalar Sadiya Farouk da Betta Edu

N585m: EFCC Ta Titsiye Akanta Janar a kan Zargin Badakalar Sadiya Farouk da Betta Edu

  • Dr. Oluwatoyin Madein ta bayyana a EFCC domin amsa muhimman tambayoyi a kan bincike da ake yi
  • Hukumar yaki da rashin gaskiya tana kokarin bankado abubuwan da suka faru a ma’aikatar jin-kai
  • Jami’an EFCC suna zargin kudin gwamnati sun yi ciwo a ma’aikatar jin-kai daga 2019 zuwa shekarar bara

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Binciken da ake yi a ma’aikatar jin-kai da yaki da talauci a kasa, ya yi sanadiyyar nemo Akanta Janar Dr. Oluwatoyin Madein.

The Nation ta kawo labari cewa binciken ya je kan Dr. Oluwatoyin Madein a matsayinta na shugaban akantocin gwamnatin tarayya.

EFCC.
EFCC tana binciken Sadiya Umar-Farouq da Betta Edu Hoto: @Sadiya_farouq, @edu_betta
Asali: Twitter

AGF: Meya kai Oluwatoyin Madein gaban EFCC?

Jami’an hukumar EFCC sun zauna da Oluwatoyin Madein ne bisa zargin dauke wasu kudi daga ma’aikatar tarayyar zuwa asusun mutane.

Kara karanta wannan

Tsohon Mataimakin Gwamnan CBN ya goyi bayan a janye wasu ofisoshi zuwa Legas

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana zargin an cire makudan miliyoyin gwamnati, aka aika zuwa akawun a bankuna.

An karkatar da kudin COVID-19?

EFCC mai yaki da rashin gaskiya ta nemi Dr. Madein tayi karin haske a kan wasu N3bn da ake zargin an dauke daga asusun COVID-19.

Hukumar kasar tana tunanin an yi amfani da kudin da aka tanada domin yaki da annobar Coronvairus, aka yi wasu ayyuka na dabam.

EFCC za ta iya sake neman OAGF

Rahoton ya ce alamu sun nuna nan gaba za a iya sake gayyato Akanta Janar din domin ta cigaba da yi wa hukumar EFCC karin haske.

Majiya ta shaida cewa an gano wasu sababbin bayanai a wajen binciken Dr. Betta Edu wanda Bola Ahmed Tinubu ya dakatar daga ofis.

Haka kuma bayanai sun kara fitowa wajen binciken Sadiya Umar-Farouq da Halima Shehu wanda ta rike shugabar tsarin NSIPA ta kasa.

Kara karanta wannan

Tunji Ojo: Gwamnati ta shiga binciken Ministanta da ake zargi a badakalar kwangila

Bayan zaman da aka yi da AGF a ranar Litinin, Business Day ta ce an bukaci ta fito da was takardu za su bayyana duk inda kudi suka shiga.

Jami’an binciken sun kuma umarci Akantar ta kawo wasiku da takardun umarnin da aka bada wajen fitar da kudi daga ma’aikatar jin-kai.

Za a adana N8tr saboda cire tallafi

A sakamakon cire tallafin man fetur da gwamnatin tarayya tayi, kuna da labari cewa an huta da kashe kimanin N4tr a kowace shekara.

Bayan haka, Taiwo Oyedele ya ce aaboda sakin darajar Naira a kasuwa, gwamnatin Bola Ahmed Tinubu za ta adana N4tr a duk shekara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng