Ministan Tinubu Ya Ki Amsa Gayyatar Hukumar Kula da Da’ar Ma’aikata

Ministan Tinubu Ya Ki Amsa Gayyatar Hukumar Kula da Da’ar Ma’aikata

  • Rahotanni sun bayyana cewa ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ola ya ki amsa gayyatar hukumar da'ar ma'aikata
  • An gano cewa hukumar CCB ta nemi Tunji-Ola ya bayyana gabanta a ranar Talata 16 ga watan Janairu don amsa tambayoyi
  • Hukumar CCB na tuhumar ministan da sa hannu a wata badakalar naira miliyan 438 da aka karkatar karkashin ma'aikatar jin kai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya yi watsi da gayyatar da hukumar kula da da’ar ma’aikata ta yi masa kan wani bincike da ake yi na zargin karya ka’idojin da’a na jami’an gwamnati.

Ministan, wanda aka shirya zai gana da jami'an hukumar da karfe 11 na safiyar Talata, bai zo ofishin ba tsakanin karfe 10 na safe zuwa 1 na rana, The Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Tunji Ojo: Gwamnati ta shiga binciken Ministanta da ake zargi a badakalar kwangila

Ministan Tinubu ya ki amsa gayyatar hukumar CCB
Ministan Tinubu ya ki amsa gayyatar hukumar kula da da’ar ma’aikata. Hoto: @officialABAT, @edu_betta, @BTOofficial
Asali: Facebook

Mai magana da yawun CCB, Veronica Kato ta tabbatar da rashin zuwan ministan a wata hira ta wayar tarho a ranar Talata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin da ya sa CCB ke neman ministan

Veronica Kato, ta ce za a sake dage sauraren karar ministan zuwa wani lokaci bayan da ya rubuta wa ofishin wasika kan cewa ya je yin waiki aiki ne.

Da aka tambaye ta game da ranar da aka saka ta gaba, ta ce babu takamaiman rana tukuna.

CCB dai ta gayyaci ministan ne kan yadda kamfaninsa ya yi kwangilar naira miliyan 438 karkashin ma’aikatar jin kai da yaki da fatara.

Wata takarda da jaridar Premium Times ta samu a ranar Litinin ya bayyana cewa CCB ta nemi ministan da ya bayyana a gabanta a ranar Talata 16 ga watan Janairu, 2024, a hedikwatar CCB da ke a sakatariyar tarayya, Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.