Tinubu, Gowon da Sauran Jiga-Jigai Sun Halarci Kaddamar da Littafin Karrama Buhari a Abuja
- An ƙaddamar da littafi mai suna ‘Aiki tare da Buhari’ domin karrama tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a Abuja
- Shugaban ƙasa Bola Tinubu, tsohon shugaban ƙasa, Janar Yakubu Gowon da sauran manyan baki ne suka halarci taron
- Tsohon mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin yada labarai Femi Adesina ne ya rubuta littafin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Taron ƙaddamar da littafin karrama tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari na jan hankalin manya da masu faɗa aji a siyasar Najeriya.
Shugaban ƙasa, Bola Tinubu, wanda shine babban baƙo na musamman, tsohon shugaban ƙasa, Janar Yakubu Gowon da Farfesa Yemi Osinbajo da sauran manyan baƙi sun hallara a Abuja domin ƙaddamar da littafin mai suna ‘Aiki tare da Buhari’.
Kamar yadda gidan jaridar Channels tv ya ruwaito, tsohon mai ba Buhari shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai Femi Adesina ne ya rubuta littafin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Uwargidan tsohon shugaban ƙasa, Aisha Buhari, shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, da wasu da dama, sun halarci bikin kaddamar da littafin.
Taron dai kusan shi ne karon farko da Tinubu da Buhari suka haɗu a fili tun bayan miƙa mulki a ranar Litinin, 29 ga watan Mayu.
Tinubu da Buhari sun haɗu a Abuja a karon farko tun ranar 29 ga Mayu
Buhari ya ziyarci Abuja a ranar Talata, 16 ga watan Janairu, ziyara ta farko tun bayan da ya miƙa mulki a ranar 29 ga watan Mayu ga magajinsa, Bola Tinubu.
Tsohon shugaban ƙasar ya ziyarci babban birnin Najeriya ne domin halartar bikin ƙaddamar da littafin da aka rubuta domin karrama shi.
A ranar Litinin, 15 ga watan Janairu, tsohon hadimin Shugaba Buhari, Bashir Ahmad ya sanar da cewa Buhari zai halarci ƙaddamar da littafin.
Tinubu Ya Hadu da Obasanjo
A wani labarin kuma, kun ji cewa a katon farko tun bayan rantsar da shi a matsayim shugaban ƙasa, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya haɗu da tsohon shugaɓan ƙasa, Olusegun Obasanjo.
Shugaba Tinubu ya haɗu da Obasanjo ne a wajen rantsar da Gwamna Hipe Uzodinma na jihar Imo, a karo na biyu bayan ya samu nasarar lashe zaɓen gwamnan jihar.
Asali: Legit.ng