Betta: Gbajabiamila Ya Amince da N2bn Ba Tare da Izinin Tinubu Ba? Fadar Shugaban Kasa Ta Yi Martani
- Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa Femi Gbajabiamila ya shiga cikin kunshi wadanda ake zargi a badakalar kudi da ake tuhumar dakatacciyar Ministar jin kai Betta Edu
- Hakan ya samo asali da yadda aka ga wata takardar amincewa da sakin kudi Naira Biliyan 3, ga ma'aikatar ta, wadda yanzu haka ke ci gaba da zagaya kafafen sada zumunta
- Takardar amincewa da diban kudin, ta fara sanya ayar tambaya a zukatan yan kasa, tare da tantanmar anya kuwa da sanin shugaban kasa wajen amince domin fitar da kudin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Abuja - Mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin labarai, Bayo Onanuga, ya yi martani kan wata takarda da aka fitar na cewa an amince da Naira biliyan 3 don tantance rajistar shirye-shirye da aka samar a zamanin gwamnatin Buhari.
Kamar yadda Business day ta rahoto, an yi zargin cewa takardar wacce ta yadu a shafukan sada zumunta, ta fito ne daga hannun shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin tarayya, Femi Gbajabiamila.
Haka kuma, an yi zargin cewa takardar ta nuna cewa Shugaban kasa Tinubu ya umurci dakatacciyar ministar harkokin jin kai, Dr Betta Edu, da ta saki naira biliyan 3 domin tantance rijistar shirin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai kuma, ana zargin cewa Gbajabiamila ya amince da kudin ne ba tare da izinin Tinubu ba.
Betta Edu: Tarin badakaloli a ma'aikatar jin kai
Sabbin zarge-zargen na zuwa ne yayin da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ke tsaka da binciken badakala a ma'aikatar jin kan.
Tun farko dai an samar da rijistan ne don shirye-shiryen bayar da tallafi ga marasa karfi.
An yi zargin cewa kamfanoni da dama sun samu kwangila daga naira biliyan 3 din da aka bai wa dakatacciyar ministar, lamarin da ya haddasa cece-kuce tare da sa shugaban kasar bayar da izinin bincike a kai.
N3bn don tantance rijista: Bayo Onanuga ya yi martani
Da yake martani kan ci gaban a ranar Litinin, 15 ga watan Janairu, Onanuga ya bukaci yan Najeriya da daure sannan su kara hakuri, yana mai gargadi kan hukuncin kafafen yada labarai.
Sai dai kuma, sabanin zargin da ake yi, Onanuga ya tabbatar da cewar Shugaba Tinubu ya amince da sakin naira biliyan 3 don tantance rijistan, rahoton Punch.
Jaridar Punch ta nakalto Onanuga na cewa:
"Shugaban kasar ya umurci EFCC da ta binciki ma'aikatar jin kai da duk wadannan batutuwa da tuni suke karkashin binciki."
“Ina da tabbacin cewa EFCC ta rigada ta ga wannan takarda daga ofishin shugaban ma’aikatan shugaban kasa kuma suna yin wani abu a kan wadannan bincike.
“Mu kyalesu su yi aikinsu. Kada mu kasance masu yin bincike sau biyu a kan magana daya, ko kuma a yi shari'ar kafofin watsa labarai kan batun da ake bincike. ‘Yan Najeriya su yi hakuri.
"Da zaran EFCC sun kammala bincikensu, za su gabatar da rahotonsu ga shugaban kasar wanda zai dauki mataki kan sakamakon binciken."
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Malamin addini ya yi hasashen tsige Gbajabimala
A wani labari na daban, Legit Hausa ta kawo a baya cewa Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual, Primate Elijah Ayodele, ya gargadi Femi Gbajabiamila, shugaban ma'aikatan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, da ya zama mai sa ido sosai.
A wani sakon gargadi da ya saki a shafinsa na X (wanda aka fi sani da Twitter a baya) a ranar Alhamis, 28 ga watan Disamba, Primate Ayodele ya bayyana cewa ya gargadi na hannun damar shugaban kasar a baya.
Asali: Legit.ng