‘Yan Bindiga Sun Koma Fada da Juna, An Tarwatsa Yaran Mashahurin ‘Dan Ta’adda
- Dogo Gide ya gamu da iyakarsa da ya hadu da sojojin ISWAP da suka hallaka yaransa da ke addabar al’umma
- ‘Dan bindigan ya nemi ya kulla alaka da mayakan Ansaru, a yanzu dai ya tashi da asarar dukiya da rashin yaransa
- Gide ya yi karfi a kauyukan da ke Babban Doga da Mai Tukunya a karamar hukumar Dansadau a jihar Zamfara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Nigeria - Rigima ake yi tsakanin kungiyoyin ta’addanci a Arewacin Najeriya, hakan ya yi sanadiyyar murkushe ‘yan bangaren Dogo Gide.
Wani rahoto da Premium Times ta fitar a farkon makon nan ya ce dakarun kungiyoyin Ansaru da ISWAP sun aukawa ‘yan bindiga.
‘Yan ta’addan da ke da alaka da Al-Ka’ida sun kashe da yawa a cikin yaran Dogo Gide, majiyar jami’an tsaro ta ce ‘dan ta’addan ya tsere.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ana murkushe mutanen Dogo Gide
An yi gwabzawar ne a farkon watan Disamban da ta gabata, yanzu babu labarin Dogo Gide wanda ya dade yana addabar jihohin Arewa.
Sojojin Ansaru da ISAWP sun saba kai hari a kan jami’an gwamnati ne. kungiyoyin ba su cika sha’awar kai hari ga Bayin Allah a kauyuka ba.
A wasu lokutan, rundunar kungiyoyin su kan takawa ‘yan bindiga burki a garuruwa. Wani ‘dan kasuwa ya shaidawa jaridar haka a Neja.
Wani da ke gudun hijira a Kureba a garin Shioro ya ce ‘yan ta’addan su kan tasa miyagun ‘yan bindiga a gaba wajen biyan kudi a kasuwa.
Dogo Gide ya koma wajen Ansaru
A yakin da aka yi a watan Yunin 2023, Gide ya rasa sojojinsa tara ga mayakan ISWAP a Kurebe, ‘danuwansa yana cikin wadanda aka kashe.
Jagoran ‘yan bindigan ya nemi yin sulhu da sojojin Ansaru ganin yadda ‘yan ISWAP suka addabe shi, amma kawancensu bai dade ba.
Yaran Gide sun hada-kai da Ansaru, da farko suka samu makamai a Agustan bara, da kayan yakin ne suka harbo jirgin sojoji a Chukuba.
Wani hali Dogo Gide suke ciki a yau?
Ba a je ko ina ba alaka tayi tsami, ‘dan bindigan ya ba shugaban Ansaru kudi har N200m domin sayen makamai, har yau shiru ake ji.
Wata majiya ta ce yanzu ‘dan bindigan bai da mayaka, manyan ‘yan ta’adda sun karya Gide shekaru da juyawa Buharin Daji baya.
Kisan manyan Najeriya a 1966
A juyin mulkin 1966, ana da labari Emmanuel Ifeajuna ya kashe Abubakar Tafawa Balewa, Zakari Maimalari da kuma Abogo Largema.
Laftanan Kanal Arthur Unegbe ne kadai ‘dan kabilar Ibo da aka hallaka a juyin mulkin.
Asali: Legit.ng