Dogo Gide: Mutumin da ya yi ajalin Buharin Daji

Dogo Gide: Mutumin da ya yi ajalin Buharin Daji

Idan mai karatu zai iya tunawa a ranar Laraba, 7 ga watan Maris ne labara ya fara bazuwa a cikin garin Zamfara na cewa fitaccen barawon shanun nan mai suna Buharin Daji ya dafa kasa, sai dai da dama basu san wanene ajalinsa ba.

Kamar yadda rahotannin suka tabbatar, Buhari Daji ne ya aika yaransa suka sato shanun surukan Dogo, inda ma suka kashe mutum biyu, wannan ne ya harzuka Dogo, inda ya nemi Buharin ya bashi shanunsa, shi kuma yaki, yace tuni ma ya rabar ma yaransa.

KU KARANTA: Kwaya ce! Wani matashi dan sara suka ya yi ma kansa yankan rago bayan ya tafka ma dan uwansa mummunar ta’asa

Daga nan ne fa Dogo Gide ya dau alwashin kashe Buharin Daji, inda ya kira wani taron sulhu da Buhari, a yayin taron ne ya dirka masa harsashi, yayin da yaransa kuma suka bude ma yaran Buharin Daji wuta, nan take suka kashe guda 8.

Dogo Gide: Mutumin da ya yi ajalin Buharin Daji
Dogo Gide a hagu

Jaridar Aminiya ta shiga ta fita wajen nemo labarin wannan bawan Allah, inda ta samo bayanai da suka nuna Dogo Gide ya kasance guda daga cikin tsoffin yaran Buharin Daji, inda daga bisani ya ci ganye, har suka zama abokan aiki.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito asalin Dogo Gide Bafulatani ne mai kiwon shanu, kuma mutumin gundunar Dansadau ne, sai dai duk jama’an yankin sun ce basu takamaimen masaniya game da garinsu Dogo Gide, amma an tabbatar da yana da mata da yara guda biyu mata.

“Dogo Gide matashi ne da shekarunsa ba su wuce arba’in ba.” Inji wani da ya san shi, ya kara da cewa a baya Dogo Gide ya kasance a cikin kungiyar barayin shanun dake cin karensu ba babbaka tare da yaran Buharin Daji, amma daga bisani ya tuba, har ma yana taimaka wa jami’an tsaro da bayannan sirri. sai dai huldarsa da jimi’an tsaron ba ta kai-tsaye ba ce, yana huldar da su ne ta hannun wadansu ’yan sa-kai.

Sai dai a yanzu haka Dogo Gide na bukatar a samu zaman lafiya a jihar Zamfara, kamar yadda mazauna kauyukan Zamfara suka tabbatar bayan wata haduwa da suka yi da shi a gonakinsu, inji wani dan kauyen mai suna Ali Hassa.

“A lokacin da mazauna kauyukan Madaka da Gajeren kauye suka hango Dogo Gide yana tafe da yaransa, sai suka tsorata kowa yayi ta kansa, amma da yazo kusa da su, sai ya bayyana musu kansa, sa’annan ya basu shawarar kowa ya cigaba da nomansa, don kuwa za a samu zaman lafiya.” Inji shi

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel