Tsohon Mataimakin Gwamna a CBN Ya Goyi Bayan Janye Wasu Ofisoshi Zuwa Legas

Tsohon Mataimakin Gwamna a CBN Ya Goyi Bayan Janye Wasu Ofisoshi Zuwa Legas

  • Kingsley Chiedu Moghalu bai ga laifi don a dauke wasu ofisoshi daga hedikwatar CBN zuwa garin Legas ba
  • Tsohon mataimakin gwamnan babban bankin kasar ya ce jama’a sun yi yawa a babban ofishin CBN a Abuja
  • Moghalu ya bada uzuri da cewa tun da aka gama ginin ofishin Legas a kusan 2012, jami’an CBN sun yi watsi da shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Ana ta kishin-kishin cewa za a maida wasu ofisoshin babban bankin Najeriya daga birnin tarayya Abuja zuwa garin Legas.

Lamarin ya jawo surutu da korafi musamman daga mutanen Arewacin Najeriya. Legit ta lura wasu suna zargin akwai makarkashiya.

Moghalu-CBN
Kingsley Moghalu yana tare da CBN Hoto: @Cenbank, kingsleymoghalu.ng
Asali: Twitter

CBN: Kingsley Moghalu ya yi magana a X

Kingsley Moghalu wanda ya yi mataimakin gwamna a bankin na CBN, ya tofa albarkacin bakinsa da yake magana a shafin X.

Kara karanta wannan

Betta Edu: Tinubu zai yi garambawul a kujerun Ministoci? Gaskiya ta fito

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mista Moghalu ya nuna yana goyon bayan wannan mataki, ya ce an yi watsi da reshen babban bankin na CBN da ke garin Legas.

Akwai laifi saboda ma'aikatan CBN sun koma Legas

Premium Times ta tabbatar da labarin, ta ce masanin tattalin arzikin bai ganin an yi laifi saboda wasu ofisoshi sun bar hedikwata.

Tsohon ‘dan takarar shugaban kasar ya kawo dalilan da za suka karfafa shirin da ake zargi shugabannin bankin CBN suna yi a yau.

Tsohon mataimakin gwamnan ya ce shi ya kaddamar da ginin CBN na Legas shekaru 12 da suka wuce, amma ba a cin moriyarsa.

CBN: Ra'ayin Kingsley Moghalu

"Ban ga wani dalilin wannan ‘tashin hankali’ ba. An gama ginin sabon ofishin CBN a Legas kuma an kaddamar shekaru kusan 12 da suka wuce lokacin ina bankin.

Kara karanta wannan

Yadda Tinubu ya warware abin da Ganduje ya so a shiryawa Kano a Kotun Koli Inji Abba

"Iyaka abin da zan iya tunawa, ba a cin moriyarsa da kyau.
"Sannan, adadin ma’aikatan da ke hedikwata a Abuja sun yi yawa duba da lafiya da tsaron ginin.
"Baya ga haka, wuraren da sassan da za su koma Legas za su rika sa ido a kai yawanci a Legas su ke.
"Saboda haka mecece matsalar? A wurina matakin ya yi daidai.”

- Kingsley Chiedu Moghalu OON

APC ta taya Bisi Akande murnar cika 85

Bisi Akande wanda ya cika shekara 85 a yau, ya taka rawar gani wajen kafa APC a 2013 kamar yadda muka ji labari a makon nan.

Muhammadu Buhari ya nemi takara sau uku bai dace ba, ya cire rai da mulki bayan 2011, a karshe ya samu shugabanci a inuwar APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng