Idan Kwankwaso Ya Ce Magoya Bayansa Su Fada Wuta, Rabin Kano Za Su Fada Wutan, In Ji Galadima

Idan Kwankwaso Ya Ce Magoya Bayansa Su Fada Wuta, Rabin Kano Za Su Fada Wutan, In Ji Galadima

  • Wani jigon jam'iyyar NNPP ya ce idan Kwankwaso ya ce magoya bayansa su fada wuta, za su fada ba tare da kayayyakin ba
  • Buba Galadima ya ce kuma rabin mutanen Kano na iya bayar da rayuwarsu akan Rabiu Kwankwaso saboda tsananin soyayya
  • Rabiu Kwankwaso shi ne tsohon gwamnan Kano kuma tsohon dan takarar shugaban kasa karkashin NNPP a zaben 2023

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Buba Galadima, wani jigon jam'iyyar NNPP ya ce idan Rabiu Kwankwaso ya ce magoya bayansa su fada wuta, to rabin mutanen Kano ne za su fada wuta.

Kwankwaso shi ne tsohon gwamnan jihar Kano kuma tsohon dan takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar NNPP a zaben 2023 da ya gabata.

Kara karanta wannan

Tsohon shugaban APC na ƙasa ya bayyana jiha 1 da zasu ƙwace daga hannun PDP a 2024

Magoya bayan Kwankwaso a Kano
Idan Kwankwaso ya ce rabin magoya bayansa su fada wuta, rabin Kano za su fada wuta, in ji Galadima. Hoto: @KwankwasoRM
Asali: Twitter

Duk inda magoya bayan darikar Kwankwaso suke, za a gansu sanye da jar hula, kuma suna kiran kansu "yan Kwankwasiyya".

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Akwai masu son bata sunan Kwankwaso - Galadima

Galadima ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da gidan talabijin na Channels TV, kuma ya bayyana Kwankwaso matsayin wanda jama'a suka aminta da shi.

Jigon jam'iyyar NNPP ya ce har yanzu Rabiu Kwankwaso ne jagoran jam'iyyar, tare da cewa duk wani yunkuri na bata masa suna ba zai yi tasiri ba, The Cable ta ruwaito.

A cewarsa:

"Idan yanzu Kwankwaso zai ce magoya bayansa su fada wuta su mutu, inda gaya maka rabin Kano ne S su fada saboda sun yarda da shi.
"Akwai wasu shugabannin jam'iyyar APC da ke biyan wasu kungiyoyi a NNPP suna kokarin bata sunan Kwankwaso, amma har yanzu sun kasa samun nasara."

Kara karanta wannan

Kotun Koli: Kwankwaso ya fadi abubuwa 2 da Abba zai tunkara tun da ya samu nasara

Yan Kwankwasiyya sun yi wa Buba Galadima martani

Buba Galadima ya yi nuni da cewa tun kafin Kwankwaso ya shiga NNPP ake kiransa da 'Madugu' da kuma 'Jagora' wanda ya isa ya zama izinina ga 'yan adawa.

Sai dai wani mazaunin karamar hukumar Bichi da ke Kano, Usman Sani Ahmad da ya zanta da Legit Hausa, ya ce ba ko shakka maganar da Buba Galadima ya yi gaskiya ne.

Usman Ahmad ya ce:

"Zan sake jaddadawa duniya cewa ba wai iya wuta kawai ba, ko ina Kwankwaso ya ce mu fada za mu fada, ba tare da wani waige ba."

Ahmad ya ce babu wani umurni da Kwankwaso zai ba magoya bayansa ba su bi ba, inda ya buga misali da lokacin da jagoran NNPP ya ce su bar tsagin gwamnati su koma adawa, kuma suka yi hakan.

Shi kuwa wani Ibrahim Mohammed da aka fi sani da 'Beware', ya ce sam ba zai iya bin umurnin wani ya shiga wuta ba.

Kara karanta wannan

APC ta sadaukar da kujerar gwamnan Kano ga Abba Kabir ne don gudun fitina? gaskiya ta fito

'Beware' ya ce suna kaunar tafiyar Kwankwasiyya ne don neman wa talaka 'yanci, amma batun Galadima na cewa za su shiga wuta saboda Kwankwaso ba gaskiya ba ne.

Kotun Koli ta yanke hukunci kan zaben gwamnan jihar Bauchi

A wani labarin, Kotun Koli ta tabbatar da cewa Bala Mohammed ne ya lashe zaben gwamna a jihar Bauchi da aka gudanar a watan Maris, shekarar 2023.

Jam'iyyar APC da dan takarar ta Sadiq Abubakar ne suka shigar da kara gaban kotun, inda suka nemi a soke zaben jihar saboda aikata laifuka da aka yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.