Badakalar Naira Miliyan 30: Kotu Ta Aika Tsohon Dan Majalisar Kaduna Magarkama

Badakalar Naira Miliyan 30: Kotu Ta Aika Tsohon Dan Majalisar Kaduna Magarkama

  • An aika tsohon dan majalisa a jihar Kaduna, Suleiman Dabo, magarkamar Kuje da ke babban birnin tarayya Abuja
  • An tura shi gidan gyara halin ne zuwa lokacin da Mai Shari'a James Omotosho na babbar kotun tarayya da ke Abuja zai yanke hukunci kan bukatar neman belinsa
  • An gurfanar da Dabo kan wasu tuhume-tuhume bakwai kan zargin damfarar wata Misis Folashade Mojeolaoluwa ta hanyar karya da sauran laifuka

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

FCT, Abuja - An garkame Suleiman Dabo, tsohon dan majalisar dokokin jihar Kaduna (Mazabar Zaria) a gidan yari na Kuje har zuwa lokacin da za a yanke hukunci kan neman belinsa.

Kamar yadda jaridar The Nation ta rahoto, Mai shari’a James Omotosho na babbar kotun tarayya da ke Abuja ne ya ba da umarnin a ranar Litinin, 15 ga watan Janairu.

Kara karanta wannan

EFCC: Kotu ta fara zaman shari'ar tsohon ministan da ake tuhuma da kwamushe dala biliyan 6

Kotu ta garkame tsohon dan majalisa a magarkama
Kotu Ta Aika Tsohon Dan Majalisa Magarkama Kan Zargin Badakalar Naira Miliyan 30 Hoto: Court of Appeal
Asali: UGC

Kan wasu laifuka ake tuhumar Dabo?

An gurfanar da Dabo kan tuhume-tuhume bakwai da rundunar yan sandan Najeriya ke yi masa kan karbar kudi naira miliyan 30 daga hannun Misis Folashade Mojeolaoluwa ta hanyar karya da sauransu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dabo da kamfanin sun damfari Misis Mojeolaoluwa kudi naira miliyan 30 a watan Oktoba da Nuwamba, 2017, ta asusun GTBank mai lamba: 0172410075 mai suna: Ohman International Venture Limited.

Wadanda ake tuhumar a kan zargin sayar da wani tarkacen jirgin ruwa mai suna ADNAN 101, sun aikata laifin ne “lokacin da ka gabatar da kanka ga Misis Folashade S. Mojeolaoluwa a matsayin mamallakin jirgin ruwan."

Wadanda ake karan biyu sun ki amsa laifin da ake tuhumarsu a kai lokacin da aka karanto masu laifin da ake tuhumarsu a kai.

Lauyan da ya shigar da kara, Mathew Omosun ya bukaci kotun da ta garkame tsohon dan majalisar a gidan yari har sai an fara shari’a.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da ƴan bindiga suka bankawa fadar fitaccen basarake wuta a Najeriya

Mai shari’a Omotosho ya ce Dabo bai halarci zaman da aka yi a baya kusan sau takwas ba, zai dauki lokacinsa ya yi nazari sosai a kan shari’ar kafin ya yanke hukunci.

Alkalin kotun ya dage zaman har zuwa ranar 5 ga watan Fabrairu, domin yanke hukunci kan neman belin Dabo, rahoton Leadership.

Kotu ta yi hukunci kan tsohon minista

A wani labarin, mun ji a baya cewa babbar kotun birnin tarayya Abuja ta ba da belin tsohon ministan wutar lantarki da ƙarafa, Olu Agunloye, kan kudi Naira miliyan 50.

Alkalin kotun, mai shari'a Jude Onwuegbuzie, shi ne ya amince da bada belin tsohon ministan a zaman ranar Alhamis, 11 ga watan Janairu, 2024, Channels tv ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng