Abba vs Gawuna: Rundunar Yan Sandan Kano Ta Fitar da Rahoton Laifuka Bayan Hukuncin Kotun Koli
- Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta fitar da rahotonta na tsaro kan sakamakon hukuncin da kotun koli ta yanke na zaɓen gwamnan jihar
- A cewar kwamishinan ƴan sandan jihar, CP Usaini Gumel, babu wani batun aikata laifuka bayan hukuncin kotun ƙolin
- Kwamishinan ƴan sandan ya yabawa al’ummar Kano bisa haɗin kan da suke bayarwa wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Kwamishinan ƴan sandan jihar Kano, Usaini Gumel, ya bayyana cewa babu wani laifi da ke da alaƙa da hukuncin da kotun koli ta yanke na tabbatar da Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Ya kuma tabbatar da cewa babu ɓarna a shaguna ko wuraren kasuwanci kafin bikin murnar ko bayan bikin murnar a faɗin jihar.
Mista Gumel ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai a Kano ranar Asabar, inda ya jaddada cewa rahotanni daga dukkan ƙananan hukumomin 44 sun nuna an gudanar da bukukuwan lami lafiya ba tare da wata barazana ga rayuka ko dukiyoyi ba, wanda hakan ya sa aka samu zaman lafiya gaba ɗaya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kamar yadda jaridar Nigerian Tribune ta ruwaito, ya bayyana cewa:
"Muna farin ciki da kowa ya yi biyayya ga shawarar da rundunar ƴan sanda ta bayar, inda aka gudanar da bikin murnar cikin kwanciyar hankali a faɗin jihar, kuma har zuwa yanzu babu wata barazana ta tsaro.”
Mista Gumel ya ƙara da cewa, an gudanar da bukukuwan ne ba tare da wata matsala da ta janyo asarar rayuka ko kadarori a ɗaukacin ƙananan hukumomin 44 ba.
CP Gumel ya jinjinawa mazauna Kano
Ya kuma yabawa mazauna jihar bisa bayar da haɗin kai ga jami'an tsaron da aka tura, inda ya jaddada rawar da suke takawa wajen tabbatar da doka da oda a jihar, rahoton Vanguard ya tabbatar.
Duk da haka, ya buƙaci al’umma da su ci gaba da taimaka wa ayyukan rundunar ta hanyar musayar bayanai masu muhimmanci da gaggawa don hana aikata miyagun laifuka da kama masu laifi.
Ya ƙara da cewa matakan tsaro da ake da su za su ba mazauna jihar damar gudanar da ayyukansu na halal ba tare da tsangwama ba.
Gawuna Ya Yi Magana Kan Hukuncin Kotun Ƙoli
A wani labarin kuma, kun ji cewa ɗan takarar gwamnan jihar Kano na jam'iyyar APC, Nasiru Yusuf Gawuna, ya yi magana kan hukuncin da kotun ƙoli ta yanke.
Gawuna ya bayyana cewa ya amince da hukuncin domin haka Allah ya so.
Asali: Legit.ng