Gwamnatin Wike Ta Rusa Shaguna, Gidajen Cin Abinci da Sauransu a Abuja

Gwamnatin Wike Ta Rusa Shaguna, Gidajen Cin Abinci da Sauransu a Abuja

  • Hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa (DRTS), a babban birnin tarayya ta fara rusa gidajen cin abinci, shaguna, da sauran gine-gine da basa bisa ka'ida a tsashoshin tasi a fadin Abuja
  • An fara aikin rusau din ne daga Area 3 da Banex Junction da ke Abuja a ranar Juma'a, 12 ga watan Janairu
  • A yankin Area 3, tawagar DTRS, tare da taimakon hukumomin tsaro sun rusa wuraren gyaran motoci da gidajen cin abinci da sauransu

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

FCT, Abuja - Hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa (DRTS), a babban birnin tarayya ta rusa shaguna, gidajen cin abinci da sauran gine-gine da basa bisa ka'ida a babban birnin tarayyar kasar, rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Tinubu ya dakatar da shirin NSIPS da gwamnatin Buhari ta kirkira

Jaridar Legit ta rahoto cewa Nyesom Wike, ministan babban birnin tarayya shi ke jagorantar mai'aikatar ta FCTA.

Gwamnatin Wike ta yi rusau a babban birnin tarayya
Gwamnatin Wike Ta Rusa Shaguna, Gidajen Cin Abinci da Sauransu a Abuja Hoto: Nyesom Ezenwo Wike - CON, GSSRS
Asali: Facebook

Kamar yadda jaridar The Nation ta rahoto, gwamnatin ta rusa wurare a Area 3 da Banex Junction, a Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A tashar Tasi na Area 3, tawagar DTRS, da taimakon hukumomin tsaro, sun rushe wani waurin wanke motoci, wajen gyaran motoci, gidan kallo, da wuraren cin abinci da sauran gine-gine da ke aiki ba bisa ka'ida ba.

Da yake jawabi, Peter Olumuji, sakataren cibiiyar kula da sashen tsaro na FCTA, ya ce:

"Ayyukan yan 'One chance' na faruwa ne idan mutane basu da amintacciyar tashar tasi da za su hau motoci.
"Mun kewaya ko'ina da jami'an DRTS; mun lura cewa yawancin tashoshin tasi cike suke da mutane da bai kamata ace suna wajen ba, kuma ba su yan tasi damar amfani da wajen.

Kara karanta wannan

Kotun Koli ta yi hukunci kan shari'ar neman kifar da gwamna APC, ta bayyana dalilai

"Amma yanzu da muka shafe gine-ginen da basa bisa ka'ida, karin motoci za su zo tashoshin, don matafiya su samu damar shiga tasi mai aminci da tsaro zuwa inda za su."

Wike zai yi rusau a Abuja

A wani labarin, mun ji cewa a matsayinsa na babban Ministan harkokin birnin tarayya na Abuja, Nyesom Wike, ya sanar da mutanen Nuwalege su tashi.

The Nation ta ce Nyesom Wike ya bukaci masu zama a yankin Nuwalege da ke kan titin hanyar filin jirgin sama su bar unguwar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng