Gwamnan PDP Ya Cire Fargaba, Ya Faɗi Waɗanda Suka Ɗauki Nauyin Kisan Bayin Allah 200 a Arewa

Gwamnan PDP Ya Cire Fargaba, Ya Faɗi Waɗanda Suka Ɗauki Nauyin Kisan Bayin Allah 200 a Arewa

  • Gwamnan jihar Filato ya fallasa gaskiya kan masu ɗaukar nauyin kisan bayin Allah a jihar a baya-bayan nan
  • Celeb Mutfwang ya ce kashe-kashen da aka a jajibirin kirsimeti ta'addanci ne kuma yana da yakinin jami'an tsaro sun san masu ɗaukar nauyi
  • Kalaman gwamnan na zuwa ne a ranar da kotun koli ta tabbatar masa da nasara a zaben 18 ga watan Maris

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Plateau - Gwamna Caleb Mutfwang na jihar Filato ya bayyana cewa ya yi amanna hare-haren da ake kai wa jihar a baya-bayan nan ayyukan ta'addanci ne.

Gwamnan na jam'iyyar PDP ya kuma yi ikirarin cewa jami'an tsaro sun san masu kitsawa da ɗaukar nauyin wannan ɗanyen aikin da ya laƙume daruruwan rayuka.

Kara karanta wannan

Ana saura awanni kadan a yanke hukunci, PDP a jihar Arewa ta mika lamarinta ga Allah, ta yi gargadi

Gwsmnan jihar Filato, Celeb Mutfwang.
Kashe-Kashen Filato ta'addanci ne, Jami'an Tsaro Sun masu Hannu in ji Mutfwang Hoto: Celeb Mutfwang
Asali: Facebook

Sama da mutane 200 ne aka kashe a hare-haren baya-bayan nan da aka kai a jihar Filato da ke Arewa ta Tsakiya yayin wasu da dama suka rasa gidajensu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake jawabi a cikin shirin 'siyasa a yau' na kafar talabijin ta Channels ranar Jumu'a, 12 ga watan Janairu, 2023, Gwamna Mutfwang ya ce:

"Abin da zan iya fada muku shi ne kashe-kashen da ake yi a Filato da kuma hare-haren da ake kai wa a ‘yan kwanakin nan ayyukan ta’addanci ne tsantsa."

Shin su wa ke ɗaukar nauyun kisan bayin Allah?

A cewarsa, magance faruwar irin haka tun farko shi ne mafi a'ala ga Najeriya kana ya yi ikirarin cewa duk masu ɗaukar nauyin ta'addancin an san su.

"Na yi imanin cewa an san masu daukar nauyin 'yan ta'adda, masu ba su kuɗaɗe da wadanda ke ba 'yan ta'adda makamai duk ba ɓoyayyun mutane bane.

Kara karanta wannan

Ganduje ya bayyana gwamnoni da 'yan majalisun tarayya da za su rungumi jam'iyyar APC

"Kuma hukumomin tsaro sun san su ko kuma suna da karfin sanin ko su waye, shiyasa muka dage cewa dole ne hukumomin tsaro su yi aikinsu, wato kare rayuka da dukiyoyi."

Kalaman nasa sun zo ne a ranar da kotun koli ta soke hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke na tube shi daga mukamin gwamna, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Yan bindiga sun tafka ɓarna a Katsina

A wani rahoton kun ji cewa Ƴan bindiga sun bankawa motar da ta ɗauko kayan ɗakin amare uku wuta, sun kashe direba da yaron motar a jihar Katsina.

Ganau ya bayyana cewa lamarin ya faru a kan titin Jibia zuwa Batsari ranar Talata lokacin da 'yan bindiga suka tare hanyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262