Tashin Hankali Yayin Da Ƴan Bindiga Suka Bankawa Fadar Fitaccen Basarake Wuta a Najeriya

Tashin Hankali Yayin Da Ƴan Bindiga Suka Bankawa Fadar Fitaccen Basarake Wuta a Najeriya

  • Wasu tsagerun ƴan bindiga sun ƙona fadar basaraken garin Isseke da ke ƙaramar hukumar Ihiala a jihar Anambra
  • Basaraken mai suna, Igwe Emmanuel Nnabuife, ya ce maharan sun lalata komai na gidan wanda ya shafe shekaru yana ginawa
  • Kwamishinan yan sandan jihar Anambra ya ce tuni suka ƙaddamar da bincike da farautar maharan da suka aikata ɗanyen aikin

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Anambra - Wasu mahara da ake zargin ‘yan Bindiga ne sun kona fadar Igwe Emmanuel Nnabuife, Sarkin garin Isseke da ke karamar hukumar Ihiala a jihar Anambra.

Wannan hari na zuwa ne mako ɗaya bayan miyagu sun yi garkuwa da tsohon direban ayarin marigayi tsohon gwamnan jihar, Chinwoke Mbadinuju a kauyen Isseke.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun bankawa motar kayan ɗakin amare 3 wuta, rayuka sun salwanta a jihar arewa

Yan bindiga sun ƙona fadar basarake a jihar Anambra.
Yan Bindiga Sun Bankawa Fadar Basarake Wuta a Jihar Anambra Hoto: PoliceNG
Asali: Facebook

Yan bindigan sun sace tsohon direban ne bayan ya yi janazar ɗan uwansa da ya mutu saboda bai biya su haƙƙinsu ba, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ce maharan sun mamaye gidansa da tsakar dare, suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi kafin daga bisa suka tasa shi zuwa maɓoyarsu da ba a sani ba.

Basaraken ya tabbatar da ƙona fadarsa

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Igwe Emmanuel Nnabuife ya ce ‘yan bindigar sun kona gidansa wanda fadarsa ke ciki.

Ya koka da cewa ba shi da wata matsala da kowa a cikin al’ummarsa wanda wataƙila zai iya sa a aikata masa wannan ɗanyen aikin.

Basaraken ya ce:.

"Gaskiya ne wasu yara maza ne suka kona fadata kuma na rasa duk abin da na yi wahala a rayuwata don samu, a halin yanzu ba ni da gida."

Kara karanta wannan

Mutane sama da 20 sun mutu yayin da jirage biyu suka yi mummunan hatsari a jihar PDP

"Komai ya tashi aiki a gidan amma na gode wa Allah da ba a yi asarar rai ba kuma ba a yi wa kowa komai ba, haka abin yake a garina Isseke."

Wane mataki jami'an tsaro suka ɗauka?

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Anambra, CP Aderemi Adeoye, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce sun fara gudanar da bincike.

A cewarsa, rundunar ‘yan sandan ta kaddamar da farautar wadanda suka aikata laifin, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Jirage biyu sun yi haɗari a Ribas

A wani rahoton kuma Wasu jiragen ruwa guda biyu sun gamu da mummunan hatsari a yankin ƙaramar hukumar Andoni ta jihar Ribas jiya Talata

Shugaban ƙaramar hukumar Andoni ya ce akalla mutane 20 suka mutu a haɗarin, ya miƙa sakon ta'aziyya ga iyalai da ƴan uwa

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262