Tinubu ya dakatar da shirin NSIPA da gwamnatin Buhari ta kirkira

Tinubu ya dakatar da shirin NSIPA da gwamnatin Buhari ta kirkira

  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da duk wasu ayyukan hukumar NSIPA da ke gudana a yanzu haka
  • Tinubu ya dauki matakin ne domin bayar da damar gudanar da cikakken bincike kan badakalar kudi da ake zargin an tafka a hukumar
  • Wannan mataki ya shafi shirin N-Power, shirin GEEP, na ciyar da yan makaranta da sauransu, haka kuma an daskarar da hanyar fitar kudi daga hukumar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da dukkan shirye-shiryen da hukumar ba da tallafin dogaro da kai ta kasa (NSIPA) ke gudanarwa, rahoton Leadership.

Daraktan labarai a ofishin Sakataren gwamnatin tarayya, Segun Imohiosen, ne ya sanar da ci gaban a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma'a, 12 ga watan Janairu.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya yi martani kan dakatar da Betta Edu, ya aika gagarumin sako ga Tinubu

Tinubu ya dakatar da shirye-shiryen hukumar NSIPA
Tinubu ya dakatar da shirin NSIP da gwamnatin Buhari ta kirkira Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Me yasa aka dakatar da ayyukan NSIPA?

A cewar Imohiosen, matakin ya kasance ne sakamkon binciken da ke gudana kan zargin badakalar kudade a hukumar da ma shirye-shiryen kansu, rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce an dakatar da gaba daya shirye-shiryen NSIPA guda hudu da suka hada da, shirin bayar da tallafin kudi ga marasa karfi, shirin GEEP, shirin N-Power da kuma na ciyar da yan makaranta na tsawon makonni shida.

Ya ce:

"Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kuma nuna matukar damuwa game da tangardar da aka samu na aiki da kuma badakalar da ke kewaye da biyan masu cin gajiyar shirye-shiryen.
“Saboda haka ya kafa kwamitin ministoci don gudanar da cikakken bincike kan ayyukan hukumar da niyar ba da shawarar yin gyare-gyare da suka dace a hukumar NSIPA.

Kara karanta wannan

Ba kamar Buhari ba, Tinubu ya dauki mataki kan yawan kashe kudade a tafiye-tafiye, ya fadi dalili

"A yayin dakatarwar nan, an daskarar da gaba daya ayyukan da suka shafi NSIPA, ciki har da taruka, biyan kudade da rijista."

Haka kuma, Shugaban kasar ya ba dukkan masu ruwa da tsaki da yan Najeriya baki tabbacin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da jajircewa wajen gudanar da wani tsari cikin gaggawa da rashin son zuciya wanda zai tabbatar da cewa, a ci gaba.

Ya ce talakawan Najeriya za su amfana da wadannan tsari da za su gabatar wanda babu son zuciya a ciki.

Me yan Najeriya ke cewa a kan wannan mataki na Tinubu?

Legit Hausa ta zanta da wasu da suke cin gajiyar shirin N-Power don jin ta bakinsu a kan wannan mataki da shugaban kasar ya dauka.

Muhammadu Abubakar ya ce:

“Wannan mataki ne mai kyau duk da cewar mu zai kawo mana karan tsaye a harkokinmu a matsayinmu na masu cin gajiyar shirin N-Power.
“Yana da kyau a gudanar da bincike da kyau domin a gano shin da gaske talakawa ne ke cin moriyar wadannan shirye-shirye ko dai yan kadan ake watsawa tsakuwa yayin da ake sama da fadi kan sauran.

Kara karanta wannan

Innalillahi: 'Yan bindiga sun buɗe wa mutane wuta a garuruwa 3, sun kashe rayuka da yawa a arewa

“Muna kira ga gwamnati da ta kamanta gaskiya da adalci bayan an kammala bincike sannan ta hukunta duk wanda ta gano yana da hannu a badakalar.”

Malama Zahra Muhammad kuma cewa ta yi:

“Gaskiya ba mu ji dadin wannan al’amari ba. Ga shi za a hukunta mu saboda laifin da wasu wawayen cikinmu suka aikata.
“Shawara ga shugaban kasa idan har aka kammala bincike aka gano gaskiya, toh kada ya kara mika ragamar wannan ma’aikata a hannun mata musamman masu karancin shekaru.
“Lamari na tafiyar da irin wannan ma’aikata ta jin kai ya kamata a samo mutum mai dattako, mai tausayin marasa shi. Ya kasance dattijo kuma namiji. Muna fatan a dawo mana da shirin da zaran an gano gaskiya. Allah ya sa a dace.”

Hukumar NSIPA ta wanke Betta Edu

A baya mun ji cewa hukumar NSIPA ta yi martani kan zargin badakalar kudi da ake yi wa ministar jin kai da kawar da talauci, Betta Edu.

Kamar yadda jaridar The Nation ta rahoto, manajan labarai na NSIPA, Jamaludeen Kabir, ya yi watsi da ikirarin da ke alakanta ministar da badakalar kudi a hukumar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng