Hotuna Sun Kayatar Yadda Sunusi Lamido Ya Jagoranci Sallar Juma'a a Legas, Bayanai Sun Fito
- An yada hotunan tsohon Sarkin Kano, Sunusi Lamido Sunusi a jihar Legas inda ya jagoranci sallar Juma'a
- Tsohon sarkin ya jagoranci sallar Juma'ar a babban masallacin Sakatariyar jihar a Alausa da ke Legas
- Rahotanni sun tabbatar da cewa Sarkin ya ziyarci jihar Legas ce don halartar taron tunawa da tsaffin sojojin Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Legas - Tsohon Sarkin Kano, Sunusi Lamido Sunusi ya jagoranci sallar Juma'a a jihar Legas.
Tsohon sarkin ya jagoranci sallar Juma'ar a babban masallacin Sakatariyar jihar a Alausa da ke Legas.
Mene dalilin Sunusi Lamido na zuwa Legas?
Lamido ya halarci masallacin ne yayin bikin tuna wa da ranar tsaffin sojojin Najeriya a jihar Legas, cewar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sunusi wanda ya rike mukamin gwamnan Babban Bankin Najeriya, CBN a mulkin tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan.
Lamido ya yi kaurin suna wurin fadar gaskiya komai dacinta a duk lokacin da ya ga ana wani abin da bai kamata ba a kasar.
Wane lamari Sunusi ya fi tsoma baki a Najeriya?
Mai Martaban ya fi tsoma baki mafi yawan lokuta a abubuwan da suka shafi tattalin arzikin Najeriya da sauran wurare da suka shafi rayuwar al'umma.
A kwanakin baya ya yi magana kan cire tallafin mai wanda tun a farkon mulkin tsohon shugaban kasa, Jonathan ya nemi a cire tallafin.
Daga bisani shugaban ya yi yunkurin cire tallafin amma ya fuskanci zanga-zanga a dukkan fadin kasar baki daya kan lamarin.
Har ila yau, hawan Bola Tinubu ke da wuya ya tabbatar da cewa ya cire tallafin man fetur a ranar 29 ga watan Mayu.
Sunusi ya fadi babbar hanyar magance matsalar fetur
A wani labarin, tsohon Sarkin Kano, Sunusi Lamido Sunusi ya bayyana hanyar dakile tsadar man fetur a Najeriya.
Sunusi ya ce rage dogaro da man fetur ce hanya kadai da zai kawo sauki wa 'yan Najeriya kuma ya karya farashin.
Tsohon Sarkin ya bayyana haka ne a ranar 19 ga watan Oktoba yayin gabatar da wata lakca a jihar Legas.
Asali: Legit.ng