Gwamnatin Tarayya Ta Fara Shirin Yin Wani Abu 1 Domin Faranta Ran Yan Najeriya a Lokacin Azumi

Gwamnatin Tarayya Ta Fara Shirin Yin Wani Abu 1 Domin Faranta Ran Yan Najeriya a Lokacin Azumi

  • Gwamnatin tarayyar Najeriya na shirin karya farashin sukari a faɗin ƙasar nan domin sauƙaƙa wa ƴan Najeriya
  • Ministar ciniki da zuba jari, Doris Uzoka, ta ce ta haɗa hannu da masana’antun da ke samar da sukari domin rage farashinsa
  • Wani bincike ya nuna cewa ana sayar da buhun sikari mai nauyin kilo 50 a farashin N60,000 zuwa N62,000

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Gwamnatin Najeriya ta fara ƙoƙarin rage hauhawar farashin sukari a ƙasar nan da kuma inganta ƙarfin kamfanonin cikin gida da ke samar da shi.

Ministar ciniki da zuba jari Doris Uzoka ce ta bayyana hakan a ranar Laraba 10 ga watan Janairun 2023, bayan ta zagaya kamfanonin sukari a Najeriya.

FG za ta rage farashin sukari
Gwamnatin ta fara kokarin fara rage farashin sukari Hoto: Aliko Dangote. and BUA Group Chairman, Abdul Samad Rabiu Credit: Bloomberg/Contributor
Asali: Getty Images

Minista ta tattauna da kamfanoni don rage farashin sukari

Kara karanta wannan

EFCC: Kotu ta fara zaman shari'ar tsohon ministan da ake tuhuma da kwamushe dala biliyan 6

Ministar ta ce ta tattauna da manyan kamfanoni a ƙarƙashin shirin farko na tsarin sukari na ƙasa a ƙoƙarin haɗin gwiwa domin rage farashin sukarin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin wata sanarwa da ta fitar, ta ce an ɗauki matakin ne da nufin sanya farashin sukarin ya yi sauƙi saboda watan Ramadan, rahoton Daily Trust ya tabbatar.

Rahotanni sun bayyana cewa ana sayar da buhun sukari mai nauyin kilogiram 50 kan kudi tsakanin N60,000 zuwa N62,000.

Ministan ciniki ta bayyana cewa:

"Batun farashin sukari yana da matukar muhimmanci domin ya shafi kusan kowane gida a Najeriya, kuma a yau, na ga wani tsari na samar da inganci.
"Mun tsaya tsayin daka wajen tabbatar da daidaiton farashin sukari, wanda yake da matukar muhimmanci ga ƴan Nijeriya, musamman a lokacin watan Ramadan, da ci gaba da samar da masana'antun sukari mai ɗorewa da bunƙasa ga kowa."

Kara karanta wannan

Dangote ya samu sabon matsayi a jerin attajiran duniya bayan arzikinsa ya karu da N227bn a sa'o'i 24

Ta ce ta ziyarci kamfanoni masu samar da sukari irin su Dangote Sugar Refinery, BUA Sugar Refinery, Flour Mills Limited Bestaf, da kamfanin Golden Sugar.

Arziƙin Dangote Ya Ƙaru

A wani labarin kuma, kun ji cewa attajirin da yafi kowa kuɗi a nahiyar Afirika, Aloko Dangote, ya samu tarin dukiya.

Dangote ya samu N227bn a cikin sa'o'i 24 wanda hakan ya sanya ya ƙara matsawa sama a cikin jerin attajiran duniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng