Dakarun Sojojin da Ke Yaki da Yan Ta'adda Ba a Ciyar da Su? Gaskiya Ta Bayyana
- Akwai rahotannin da aka yi ta yaɗa wa kan cewa dakarun sojojin da ke yaƙinda ƴan ta'adda a Zamfara ba su samun abinci
- Rundunar sojojin Najeriya ta fito ta musanta waɗannan rahotannin waɗanda ta bayyana a matsayin ƙarya tsagwaronta
- Rundunar ta kuma buƙaci jama'a da su yi da rahotannin ƙarairayin da ake yaɗa wa domin ɓata mata suna
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Zamfara - Rundunar Sojojin Najeriya ta bayyana wasu rahotannin da ke yawo kan rashin ciyar da sojoji musamman na Operation Hadarin Daji da ke yaƙi da ta'addanci a Zamfara a matsayin ƙarya.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun mai magana da yawun runduna ta takwas, Laftanar Kanal Ikechukwu Eze.
Wane martani rundunar ta yi?
A cikin sanarwar ya bayyana cewa rahotannin da ake yaɗa wa kan rashin ba sojojin abinci da alawus ɗinsu na watan Disamba babu ƙamshin gaskiya a cikinsu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wani ɓangare na sanarwar na cewa:
"Yana da kyau a bayyana cewa saɓanin iƙirarin rashin ciyar da sojoji, babban kwamandan runduna ta takwas, wanda ke kan gaba wajen gudanar da ayyukan kakkaɓe ƴan ta'adda a jihar Zamfara, waje ɗaya yake cin abinci tare da sojojin.
"Muna kira ga jama’a da su yi watsi da duk ƙarairayin da suka shafi ciyar da sojojin mu a jihar Zamfara domin ana hakan ne domin kawo ruɗani da rashin jituwa a tsakanin dakarun Operation Hadarin Daji da suka samu nasarori masu yawa a yakin da ake yi da ta’addanci da ƴan bindiga a Zamfara."
Yaushe za a ba sojojin haƙƙinsu?
Sanarwar ta kuma ƙara wa da cewa kuɗaɗen alawus na sojojin na watan Disamba, ana aiki a kansu kuman nan ba da jimawa ba za a ba su haƙƙinsu.
Sanarwar ta yi nuni da cewa rundunar sojojin ta yaba da goyon bayan da take samu, inda ta bayar da tabbacin ci gaba da aiki tuƙuru domin wanzar da zaman lafiya da tsaro a Zamfara da Arewa maso Yammacin Najeriya.
Tinubu Ya Amince a Biya Iyalan Sojojin da Suka Mutu N18bn
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince a biya iyalan sojojin da suka rasa ransu haƙƙoƙinsu.
Shugaban ƙasar ya amince da a fitar da N18bn domin biyan haƙƙoƙin sojojin da suka riga mu gidan gaskiya.
Asali: Legit.ng