Abinda Ya Sa Aka Yi Musayar Wuta a Hanyar Kaduna Zuwa Abuja, Yan Sanda Sun Magantu
- Game da rahotannin da ake yadawa na cewar 'yan bindiga sun sace mutane a hanyar Kaduna zuwa Abuja, rundunar 'yan sanda ta ce karya ne
- A wata sanarwa da ta fitar a ranar Laraba, rundunar ta ce an yi musayar wuta tsakanin 'yan bindiga da 'yan sanda ne kawai
- Rahotanni sun bayyana cewa akalla mutum 6 ne suka ji raunuka daban daban sakamakon barin wutar da aka yi a ranar 6 ga watan Janairu
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Jihar Kaduna - Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta ce ba gaskiya ba ne rahoton da ake yadawa na zargin sace matafiya a hanyar Kaduna zuwa Abuja a ranar 6 ga watan Janairu.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar Mansir Hassan ya fitar ranar Talata a Kaduna.
Gaskiyar abin da ya faru a hanyar Kaduna zuwa Abuja
A cewar Hassan:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“An yi musayar wuta a hanyar Kaduna zuwa Abuja tsakanin jami’an tsaro da ‘yan bindiga a ranar 6 ga watan Janairu da karfe 23:30.
“Musayar wutar ta faru ne a lokacin da ‘yan bindiga da dama suka yi yunkurin tsallaka titin Dogon Fili zuwa Jere, inda jami'an tsaro suka mamaye su."
Ya ci gaba da cewa:
“Rundunar ‘yan sanda tana kira ga jama’a da ke kusa da wannan wajen da su kai rahoton duk wanda suka gani da raunin harsashi ga ofishin ‘yan sanda mafi kusa."
Yan sanda sun gargadi 'yan jarida kan wallafa labari mara tushe
A cewar jami'in, matafiya shida sun samu raunuka daban-daban na harsashi a yayin artabun, kuma an garzaya da su asibiti domin kula da lafiyarsu, Premium Times ta ruwaito.
Hassan ya ce kwamishinan ‘yan sanda, Mista Ali Dabigi, ya bukaci ‘yan jarida da su rika tantance labaransu ga jami’an tsaro kafin su buga shi.
Leadership ta ruwaito rundunar na yin kira ga jama'a da su yi watsi da labarin da aka yada na an yi awon gaba da mutane wanda ya haifar da tsoro a zukatansu don ba gaskiya ba ne.
Yan bindiga sun dauke mutane a wani rukunin gidaje a Abuja
A wani labarin kuma, 'yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun shiga rukunin gidajen Sagwari a Abuja, inda suka yi awon gaba da mutum 10.
An ce masu garkuwar sun kai farmakin da misalin karfe 7:30 na yammacin ranar Lahadi, bayan da suka fara yi wa masu gadin rukunin gidajen dukan kawo wuka tare da daure su.
Asali: Legit.ng