Hadimin Buhari Ya Sake Fada Wa Matsala Kan Dalili 1 Tak, Ya Magantu Kan Zarge-Zargen da Ake Masa

Hadimin Buhari Ya Sake Fada Wa Matsala Kan Dalili 1 Tak, Ya Magantu Kan Zarge-Zargen da Ake Masa

  • Da alamu mukarraban tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ba sa jin dadin wannan mulki na Shugaba Tinubu
  • Hadimin Buhari, Ita Enang shi ma ya na fuskantar shari’a bayan zargin bata wa tsohon gwamnan Akwa Ibom suna
  • Tsohon Gwamna Udom Emmanuel na zargin Enang da bata masa suna wanda har ya yi tasiri a rayuwarsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – Hadimin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, Sanata Ita Enang ya gurfana a gaban Babbar Kotun Tarayya kan zarginsa da ake yi.

Tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom, Udom Emmanuel shi ya maka Enang a gaban kotun kan kokarin bata masa suna, cewar Tribune.

Hadimin ya shiga halin ni 'ya su yayin da aka maka shi a kotu
Hadimin Buhari ya gurfana a gaban kotu don amsa tuhumar da ake masa. Hoto: Udom Emmanuel, Ita Enang.
Asali: Facebook

Me ake zargin hadimin Buhari?

Kara karanta wannan

Ana tsaka da ganawa kan matsalar tikitin Musulmi da Musulmi, Tinubu ya nada dan Arewa babban mukami

Udom ya zargi Ita da neman zubar masa da kima inda ya ce mulkin da ya yi a jihar shi ne mafi muni a tarihin Najeriya gaba daya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai Enang ya musanta zargin inda ya kalubalnci Udom kan shigar da shi kara da ya yi a gaban kotun.

Tsohon gwamnan a bangarenshi ya bukaci kotun ta dauki mataki inda ya ce cin zarafi da kuma bata suna da Enang ya yi ya ruguza masa kima a idon duniya.

Ya ce wannan karyar da ya yi a a ranar Asabar 29 ga watan Disambar 2018 a Legas har yau ya na ci gaba da ruguza masa rayuwa da siyasar shi.

Mene martanin hadimin Buhari?

Ya kuma bukaci kotun ta umarci wanda ake zargin ya biya shi diyyar naira biliyan daya kan ruguza masa martaba a idon duniya.

Kara karanta wannan

Tsohon sanatan APC ya bayyana dalili 1 da zai hana yan Najeriya karanta littafin Buhari

Yayin da ya ke mai da martani ta bakin lauyansa, Mba Ukweni ya kalubalanci sahihancin karar da ake masa, ThisDay ta tattaro.

Ya ce babu wasu wadanda shari’ar ta shafa da aka shigar cikin karar kamar gidan rediyon da Enang ya yi hirar.

Mai Shari'a, Olukayode Adeniyi ya dage ci gaba da sauraran karar har zuwa 5 ga watan Maris mai zuwa.

Ministar Buhari ta samu beli bayan zargin badakala

A wani labarin, Ministar Buhari, Sadiya Umar Farouk a karshe ta samu beli daga hukumar EFCC a birnin Tarayya Abuja.

Hukumar ta shafe awanni 12 ta na tatsar bayanai daga tsohuwar Ministar inda a karshe suka bayyana dalilin sake ta kan beli.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.