Masarautar Saudiyya ta bai wa Yarima Bin Salman mulkin Makkah da Madina
- Likafar Yarima Muhammed bin Salman ta cigaba
- Mun samu cewa an mika masa mulkin Makkah da Madina kungurungu
- Kafar yada labarai ta kasar Saudiyya ta sanar da hakan
Labarin da muke samu daga kafar yada labarai ta kasar Saudiyya ta sanar da cewa yanzu dai kam sarkin kasar ya mika wa dansa, mai jiran gado Yarima Muhammed bin Salman akalar mulkin garuruwan Makkah da Madina dungurungu.
KU KARANTA: 'Yan sabuwar PDP sun gindaya sharudda 4 na tsayawa a APC
Mun dai samu cewa an tabbatar da cewa, akokarin sarkin na Saudiyya na ya baiwa dan na sa mukami mai tsoka, ya dauki matakin kirkiro wani sabon mukami mai taken "Majalisar masarautar Saudiyya mai kula da Makkah da tsarkakkun wurare".
Yanzu dai an mika wa Yarima Bin Salman din shugabancin majalisar.
A wani labarin kuma, Rahotannin da muke samu daga majiyoyin mu na tabbatar mana da cewa za a ci gaba da shirin taron kolin da aka shirya za'a yi tsakanin shugaban kasar Amurka Donald Trump da takwaran sa na kasar Koriya ta Arewa Kim Jong-un a Singapore ranar 12 ga watan Yuni.
Wannan labarin dai na zuwa ne 'yan kwanaki kadan bayan shugaban na Amurka ya soke taron a wani yanayin da ya jefa hankulan manyan jami'an diflomasiyya na duniya cikin fargaba da rudani.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng