Majalisar Dinkin Duniya Ta Yi Magana Kan Farashin Fetur a Najeriya, Ta Fadi Abin da Zai Faru a 2024
- Majalisar Dinkin Duniya ta ce Najeriya za ta fuskanci rage farashin man fetur a shekarar 2024
- Majalisar Dinkin Duniya ta ce saboda karuwar karfin tace man fetur a kasar, akwai yiwuwa farashin fetur zai ragu a wannan shekarar
- Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ‘yan kasuwar man fetur da kuma NNPC suka ce babu wani shiri na kara farashin man fetur
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Majalisar Dinkin Duniya ta yi hasashen faduwar farashin man fetur a Najeriya a shekarar 2024.
Majalisar UN a cikin rahotonta na yanayin tattalin arzikin duniya (WESP) na shekarar 2024 ta bayyana cewa Najeriya za ta samu karin karfin tace danyen mai a cikin gida
Matatun mai na gida za su rage farashin man fetur a Najeriya
Rahoton ya ce kara karfin tace mai a cikin kasar na iya rage farashin mai a shekarar 2024 da kuma wasu shekarun a gaba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, sashen UN DESA tare da hadin gwiwar sashen UNCTAD da kuma kwamitocin shiyya biyar na Majalisar Dinkin Duniya sun yi hasashen samun karuwar tattalin arzikin Najeriya daga kashi 2.9% zuwa kashi 3.1% a 2024
Rahoton ya nuna karuwar ci gaban Najeriya a 2024 ya dogara ne da sauye-sauyen manufofin gwamnati a shekarar 2023, musamman a bangaren samar da makamashin lantarki.
Kamfanin NNPC da dillalan mai sun yi magana kan farashin man fetur
Wannan ci gaban dai na zuwa ne a daidai lokacin da kamfanin mai na Nigeria da kungiyar dillalan man (IPMAN) suka ce babu wani shiri na kara farashin man fetur a Najeriya.
IPMAN ta ce rahotannin da ake yadawa na karin farashin man fetur ba su da tushe balle makama duk da faduwar Naira da kuma karancin kudaden waje na shigo da fetur din.
Kamfanin NNPC ya bayyana cewa babu wani rikici tsakaninsa da ’yan kasuwar kan farashin man fetur a Najeriya, Channels TV ta ruwaito.
Abin da IPMAN ta ce game da kara farashin man fetur a Najeriya
A jiya Talata, muka kawo maku rahoton wata sanarwa da kungiyar dillalan man fetur ta Najeriya (IPMAN) ta fitar, inda ta fadi matsayarta ta karshe kan batun karin kudin mai.
A cewar IPMAN, kamfanin NNPC ne kadai ke shigo da mai cikin kasar, don haka shi kadai ne zai iya rage wa ko kara kudin man ba wai 'yan kasuwa ba.
Asali: Legit.ng