Innalillahi: Babban Malamin Addinin Musulunci Ya Rasu Ya Na da Shekaru 101, Tinubu Ya Tura Sako

Innalillahi: Babban Malamin Addinin Musulunci Ya Rasu Ya Na da Shekaru 101, Tinubu Ya Tura Sako

  • Shugaba Tinubu ya kadu da samun labarin rasuwar Adinni na Legas, Sheikh Abdul-Afis Aṣamu Abou a jihar
  • Marigayin ya rasu a daren jiya Talata 9 ga watan Janairu ya na da shekaru 101 a duniya bayan fama da jinya
  • Rahotanni sun tabbatar cewa za a yi sallar jana'izarsa da misalin karfe 2 na rana a babban masallacin Juma'a a Legas

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Legas - Shugaban kwamitin babban masallacin Juma'a a Legas, Sheikh Abdul-Afis Aṣamu Abou ya rasu.

Marigayin Baba Adinni na Legas ya rasu a daren jiya Talata 9 ga watan Janairu ya na da shekaru 101.

Babban malamin addinin Musulunci ya rasu a Legas da shekaru 101
Marigayin ya rasu ne a daren jiya Talata a jihar Legas. Hoto: Bola Tinubu, Baba Adinni of Lagos.
Asali: Twitter

Yaushe marigayin ya rasu?

The Nation ta tattaro cewa za a yi sallar jana'izarsa da misalin karfe 2 na rana a babban masallacin Juma'a a Legas.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Shahararren malamin addinin Musulunci ya rasu ya na da shekaru 80 a duniya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaba Tinubu ya nuna alhininsa kan wannan babban rashi da aka yi a jihar Legas.

Tinubu ya tura sakon jaje ga iyalan marigayin da al'ummar Musulmi a Legas da ma gwamnatin jihar baki daya.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakinsa, Ajuri Ngelale ya fitar a yau Laraba 10 ga watan Janairu.

Sanarwar ta ce marigayin ya ba da gudunmawa sosai wurin tabbatar da zaman lafiya da ba da gudunmawa ga al'ummar Musulmai a Legas.

Mene Tinubu ke cewa kan rasuwar?

Sanarwar ta ce:

"Baba ya sadaukar da rayuwarsa wurin ba da gudunmawa ga al'umma, ya yi rayuwa mai inganci kuma cikin kan-kan da kai.
"Rayuwar Baba abin koyi ne ga dukkan al'umma wanda za mu yi kewarsa matuka saboda irin kyawawan halayensa."

Tinubu ya yi addu'ar ubangiji ya kai rahama kabarinsa tare da ba shi aljanna firdausi madaukakiya.

Kara karanta wannan

Shehu Sani ya yi martani yayin da Tinubu ya dakatar da Betta Edu, ya yi shagube ga Buhari

Babban malamin Musulunci ya rasu a Ibadan

A wani labarin, Allah ya karbi rayuwar babban malamin addinin Musulunci a Ibadan, Sheikh Abdulfatai Muhali Alaga a jihar Oyo.

Alaga ya rasu ne da safiyar jiya Talata 9 ga watan Janairu ya na da shekaru 80 bayan ta sha fama da jinya.

Gwamna Seyi Makinde ya tura sakon jaje ga iyalan marigayin inda ya yi addu'ar ubangiji ya masa rahama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.