An Bindige Dan Tsohon Dan Majalisar Wakilan Najeriya a Amurka
- An harbe har lahira ɗan Honorabul Ehiozuwa Agbonayinma, Osazuwa Agbonayinma, a ƙasar Amurka
- Mahaifin nasa ne ya tabbatar da rasuwar Osazuwa, wanda har yanzu bai bayar da cikakken bayani kan yadda ɗansa ya rasu ba
- Osazuwa mawaƙi ne ɗan Najeriya da ke zaune a Amurka wanda aka fi sani da Zuwa daga ƙungiyar mawaƙa ta Roze
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Ƙasar Amurka - Osazuwa Agbonayinma, wani mawaƙi ɗan Najeriya dake zaune a ƙasar Amurka, da aka fi sani da Zuwa kuma mamba a ƙungiyar mawaƙan Roze, ya rasa ransa a ƙasar Amurka.
Jaridar Channels tv ta ce har yanzu babu cikakkun bayanai kan mutuwarsa, amma mahaifinsa, tsohon ɗan majalisar wakilai a Najeriya, Ehiozuwa Agbonayinma, ya tabbatar da harbe ɗan nasa.
Ya bayyana cewa an harbe ɗansa ne a bayan kansa a ranar Lahadin da ta gabata, rahoton Sahara Reporters ya tabbatar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Osazuwa ƙwararre ne a fannin waka wanda ya yi digiri na biyu a fannin gine-gine.
Zuwa, wanda tare da ɗan uwansa Eghosa, suka kafa ƙungiyar mawaƙan Roze, sun samu karɓuwa saboda waƙoƙinsu, musamman waƙar 'Ileke' da ta samu karɓuwa a shekarar 2020.
A shekarar 2018, mawaƙan biyu suka saki faifan bidiyon waƙarsu ta farko mai suna 'The Whole Night'.
An bindige minista har lahira
A baya kun ji cewa wani mai tsaron lafiyar ƙaramin ministan ƙwadago, samar da ayyukan yi da harkokin masana'antu na ƙasar Uganda, Kanal Charles Okello Engola, ya bindige shi har lahira.
Sojan dai ya yi wannan ɗanyen aikin ne lokacin da ministan yake ƙoƙarin shiga motarsa domin tafiya wurin aiki.
Jami'in sojan wanda ya yi ƙorafin rashin kyautata masa da rashin biyansa haƙƙinsa, ya kuma bindige kansa har lahira.
Ɗalibi Ya Bindige Malamar Makaranta a Amurka
A baya rahoto ya zo cewa wani ɗalibin makarantar firamare mai shekara shida a duniya ya bindige malamarsa a jihar Virginia da ke ƙasar Amurka.
Ɗalibin ya harbi malamar ne mai shekara 30 inda ta samu raunuka bayan ya buɗe wuta a cikin aji.
Asali: Legit.ng