Matafiya 8 Sun Rasa Ransu Bayan Yan Ta'adda Sun Saka Bam a Kan Hanya a Jihar Borno

Matafiya 8 Sun Rasa Ransu Bayan Yan Ta'adda Sun Saka Bam a Kan Hanya a Jihar Borno

  • An samu asarar rayukan bayan Allah a jihar Borno bayan motocinsu sun taka nakiyoyi suna tsaka da tafiya a jihar Borno
  • Aƙalla rayukan mutum takwas ne suka salwanta bayan motocin sun taka nakiyoyin a kan hanyar Ngala zuwa Dikwa
  • Mutane da dama sun samu munanan raunuka yayin da motocin guda biyu suka yi lalacewar da ba za su gyaru ba

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Borno - Aƙalla mutum takwas ne ake fargabar sun rasa rayukansu, wasu da dama kuma sun samu raunuka daban-daban a jihar Borno.

Lamarin ya auku ne lokacin da wasu motoci biyu na kasuwanci suka taka nakiyoyi a kan hanyar Ngala zuwa Dikwa a ƙaramar hukumar Ngala ta jihar Borno.

Kara karanta wannan

Hankula sun tashi bayan yan bindiga sun halaka babban basarake a gidansa

Bam ya halaka matafiya a Borno
Bam ya tashi da motocin matafiya a Borno Hoto: @GovBorno
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 10:30 na safe a kusa da ƙauyen Kinewba da ke Ngala.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni sun ce an kai harin na nakiya ne a nisan kilomita 15 daga Maiduguri, babban birnin jihar.

Yadda lamarin ya auku

Wani majiyar tsaro ya bayyana cewa motocin biyu da lamarin ya shafa sun yi lalacewar da ba za a iya gyara su ba.

A kalamansa:

"Motocin sun bar Ngala ne da misalin ƙarfe 9:000 na safe yayin da lamarin ya faru a nisan kilomita 15. Fararen hula takwas ne ake fargabar sun mutu ciki har da ƙananan yara biyu, sannan wasu da dama sun samu munanan raunuka sakamakon fashewar nakiyoyin."

Wata majiya mai ƙarfi ta Civilian JTF ta ce motocin biyu ƙirar Izuzu da wata babbar mota ce suka taka bam ɗin kuma ana fargabar kusan dukkan fasinjojin sun mutu.

Kara karanta wannan

Innalillahi: 'Yan bindiga sun buɗe wa mutane wuta a garuruwa 3, sun kashe rayuka da yawa a arewa

A kwanaki biyu da suka wuce ne dai Gwamna Babagana Zulum ya bi hanyar lokacin da ya kai ziyarar jin ƙai zuwa Ngala.

Ƴan Boko Haram Sun Halaka Mutane a Chibok

A wani labarin kuma, kun ji cewa mayaƙan Boko Haram sanye da kayan sojoji sun kai farmaki a ƙauyukan Chibok da ke Borno.

Ƴan ta'addan a yayin farmakin sun halaka mutum 12 a ƙauyukun Gamatarwa da Tsiha na ƙaramar hukumar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng