Kwanaki Kadan Bayan Samun Matsala a Afirka, Dangote Ya Sake Sabon Matsayi, Ya Ci Kazamar Riba
- Alhaji Aliko Dangote ya sake karbe matsayinsa a matsayin wanda ya fi kowa kudi a Nahiyar Afirka baki daya
- Dangote ya samu karuwar kudi har dala biliyan 10 a ranar 8 ga watan Janairu idan aka kwatanta da dala biliyan 9.5 a wancan makon
- Wannan na zuwa ne makwanni kadan bayan attajirin ya rasa matakinsa na wanda ya fi kowa arziki a Nahiyar
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Shahararren dan kasuwa a Najeriya, Aliko Dangote ya sake komawa matsayinsa na wanda ya fi kowa kudi a Nahiyar Afirka.
Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan attajirin ya rasa matakinsa na wanda ya fi kowa arziki a Nahiyar.
Yaushe Dangote ya rasa matsayinsa a Afirka?
Dangote ya rasa matakin nasa bayan dan kasar Afirka ta Kudu, Johann Rupert ya karbe matsayin a wurin attajirin da ke rike da matsayin tun da jimawa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kamar yadda rahoton Forbes ta tabbatar, Dangote ya samu karuwar kudi har dala biliyan 10 a ranar 8 ga watan Janairu.
Aliko Dangote ya kwace kujerar daga hannun Rupert wanda ya rike matsayin a kasa da mako daya inda hakan ya jawo cece-kuce a Najeriya.
Nawa Dangote ya mallaka a yanzu a Afirka?
A ranar 8 ga watan Janairu Rupert ya na da akalla dala biliyan 10 idan aka kwatanta da dala biliyan 10.7 a ranar 30 ga watan Janairun 2023.
A halin yanzu, Dangote ya na matakin 191 a duniya yayin da Rupert ke matakin 197 a fadin duniya baki daya.
Attajirin Najeriya ya ci gaba da rike matsayin wanda ya fi kowa kudi a Afirka da dala biliyan 15.5, cewar rahoton Bloomberg.
Dangote ya rasa matsayinsa a Nahiyar Afirka
A wani labarin, Attajirin dan kasuwa, Alhaji Aliko Dangote ya rasa matakin kasancewa wanda ya fi kowa kudi a Afrika.
Johann Rupert shi ya karbe matsayin da ribar dala biliyan 10.3 idan aka kwatanta da na Dangote da ke da dala biliyan 9.5.
A yanzu attajirin ya karbe matsayinsa na wanda ya fi kowa arziki a Nahiyar ta Afirka gaba daya.
Asali: Legit.ng