EFCC Ta Sanar da Matakin da Za Ta Dauka da Godwin Emefiele Ya Yi Nasara a Kotu

EFCC Ta Sanar da Matakin da Za Ta Dauka da Godwin Emefiele Ya Yi Nasara a Kotu

  • EFCC mai yaki da rashin gaskiya a Najeriya ba ta ji dadin gaskiyar da kotu ta ba Godwin Emefiele ba
  • Alkalin kotun tarayya ya ce an sabawa doka da hakkin ‘dan kasa da aka tsare tsohon gwamnan CBN
  • Mai magana da bakin hukumar EFCC ya ce za su daukaka kara domin babu ka’idar da aka saba

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Hukumar EFCC ta fitar da jawabi na musamman bayan hukuncin kotun tarayya a shari’arta da Godwin Emefiele.

Godwin Emefiele ya dauki tsawon lokacin yana fama da EFCC tun da ya bar ofis.

Mr. Godwin Emefiele
Kotu ta ce EFCC ta biya Godwin Emefiele N100m Hoto: www.efcc.gov.ng, Getty
Asali: UGC

Hukuncin da kotun da ke zama a garin Abuja ta yanke bai yiwa EFCC dadi ba, hukumar ta sanar da haka a dandalin X.

Kara karanta wannan

Badakalar N2.3tr: Betta Edu za tayi gaba da gaba da EFCC bayan Tinubu ya ajiye sanayya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

EFCC za ta biya Emefiele N100m?

Sanarwar da EFCC ta fitar a jiya ya bayyana cewa za a daukaka kara a kotun gaba da nufin soke hukuncin Alkali O.A. Adeniyi.

Mai shari’a O.A. Adeniyi ya ce tsare Godwin Emefiele da jami’an EFCC su kayi ya sabawa doka kuma an keta alfarmarsa.

Hukumar EFCC ta ce kuskure kotu tayi

Amma kakakin EFCC na kasa, Dele Oyewale ya ce kotu tayi kuskure wajen yin hukunci har da ba Emefiele diyyar kudi.

Hukumar yaki da rashin gaskiyar ta ce ba ta cafke tsohon gwamnan na CBN ba sai da ta samu cikakken izini a wajen kotu.

Jawabin Kakakin EFCC

"Hukumar EFCC ta nuna takaicinta a kan hukuncin kotun tarayya da ke birnin Abuja da ya ce a biya N100m ga tsohon gwamnan babban bankin CBN, Godwin Emefiele.

Kara karanta wannan

EFCC ta fitar da karin bayani a kan binciken daloli da aka yi a babban ofishin Dangote

"A ranar Litinin, 8 ga watan Junairu 2024, Alkali O.A. Adeniyi ya ci tarar hukumar bayan ya ce tsare Emefiele wajen yin bincike ya keta alfarmarsa na ‘dan kasa.
"Matakin bai yi la’akari da cewa an rike tsohon shugaban na CBN ne da halataccen izinin kotu ba.
"A dalilin haka, hukumar za ta dumfari kotun daukaka kara domin ayi watsi da hukuncin."

- Dele Oyewale

Ministan gida ya ce ba zai je EFCC ba

Ana da labari Olubunmi Tunji-Ojo bai so a alakanta shi da Betta Edu wanda Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da ita daga aiki a ranar Litinin.

Betta Edu da ake bincike ta ba kamfanin da Ministan gida ya kafa kwangilar miliyoyin kudi, Tunji Ojo ya ce ya yi murabus tun 2019.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng