Ba da ni ba: Minista Ya Fitar da Kan Shi Daga Zargin Karbar N438m a Hannun Betta Edu
- Olubunmi Tunji-Ojo ya tabbatarwa ‘yan Najeriya cewa bai da alaka da kamfanin New Planet Project Limited
- Ministan harkokin gidan kasar ya ce tun 2019 ya yi murabus daga kamfanin na sa da zai nemi takarar majalisa
- Ana zargin Betta Edu wanda aka dakatar daga aiki ta ba New Planet Project Limited kwangilar N438m
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - Ministan harkokin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya karyata zargin da ake yi masa na karbar kwangila daga ma’aikatar jin-kai.
A wata hira da aka yi da shi a tashar Channels a ranar Litinin, Hon. Olubunmi Tunji-Ojo ya nesanta kan sa daga zargin sabawa doka.
EFCC za ta binciki Olubunmi Tunji-Ojo?
Rahotanni a baya sun zo cewa kamfanin Ministan mai suna New Planet Project Limited ya samu kwangilar N438m a gwamnati.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ministan ya yi gaggawar musanya wannan ne ganin an dakatar da takwararsa, Dr. Betta Edu daga kujerar Ministar jin-kai ta kasa.
Yanzu haka hukumar EFCC za ta binciki Betta Edu a kan zargin badakalar N535m a ofis.
Tunji-Ojo bai ci kudin kwangila ba
Tunji-Ojo ya ce bai da wata alaka a yanzu da kwangilar da ake tunanin ya yi wa ma’aikatar jin-kai aiki, har aka biya shi N430m.
Ana zargin kamfanin New Planet Project Limited yana cikin wadanda su ka samu aiki a kwangilolin N3bn da ma’aikatar ta bada.
New Planet Project Limited da wasu kamfanoni sun yi wa gwamnatin tarayya auju wajen tattaro sunayen marasa hali a Najeriya.
"Na bar New Planet Project tuni" - Minista
Da yake kare kan shi a gidan talabijin, Tunji-Ojo ya ce shi ya kafa kamfanin shekaru goma da su ka wuce, amma ya sauka a yanzu.
A cewarsa ya yi murabus ne a 2019 da zai nemi takarar ‘dan majalisar wakilan tarayya a Ondo, The Cable ta fitar da labarin jiya.
‘Dan siyasar ya nuna takardar murabus daga kamfanin domin ya shaidawa duniya a yanzu bai da alaka da New Planet Project Ltd.
EFCC ta na binciken ma'aikatar jin kai
A makon nan EFCC ta taso Sadiya Umar Farouq domin yi mata tambayoyi a hediwatarta a Abuja a kan zargin badakalar 37bn.
Kafin nan Shugaban kasa ya dakatar da Halima Shehu bisa zargin karkatar da wasu miliyoyi a NSIPA a karkashin ma’aikatar jin-kai.
Asali: Legit.ng