Tsohon Gwamnan Babban Banki CBN Ya Samu Nasara Kan Tinubu, Kotu Ta Umarci a Ba Shi N100m

Tsohon Gwamnan Babban Banki CBN Ya Samu Nasara Kan Tinubu, Kotu Ta Umarci a Ba Shi N100m

  • Babbar kotun Abuja ta yanke hukunci kan ƙarar tauye haƙƙin ƴancin walwala da tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele ya shigar
  • Alkalin kotun ya bayyana garƙame Emefiele na tsawon wata 5 da hukumomi suka yi a matsayin wanda ya saɓa wa doka
  • Ya kuma ci tarar N100m kan gwamnatin tarayya da EFCC saboda tauye haƙƙin Emefiele tare da umarnin hana sake kama shi

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Wata babbar kotun birnin tarayya Abuja ta bayyana tsare tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele a matsayin saba wa doka.

Ƙotun ta ayyana tsarewar da wasu hukumomin gwamnatin tarayya suka yi wa Mista Emefiele na tsawon watanni biyar a matsayin haramtacce a tanadin doka.

Kara karanta wannan

Betta Edu: Jerin Muhimman abubuwa 10 da ya kamata ku sani game da Ministar da Tinubu ta dakatar

Tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele.
Tsohon Gwamnan CBN, Emefiele Ya Samu Nasara a Kotun Abuja Hoto: Godwin Emefiele
Asali: Twitter

Mai shari'a Olukayode Adeniyi, shi ne ya yanke wannan hukuncin ranar Litinin, 8 ga watan Janairu, 2024 a Abuja, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Alkalin ya ce babu wata doka da ta bai wa gwamnati ko wasu hukumomi damar tsare cikakken ɗan kasa har ya zarce wa'adin da kundin tsarin mulki ya tanada.

Kotun ta yi wannan hukunci ne a ƙarar da Emefiele ya shigar da FG, Antoni Janar na ƙasa, EFCC da shugabanta bisa tuhumar tauye masa haƙƙinsa na walwala.

Mai shari’a Adeniyi ya ce wadanda ake kara sun take hakkin Emefiele, wanda kundin tsarin mulkin ya ba shi a lokacin da suka tsare shi daga ranar 13 ga Yuni, 2023 zuwa ranar 8 ga Nuwamba, 2023.

A cewarsa, waɗanda ake ƙarar sun tsare tsohon gwamnan CBN na tsawon wannan lokaci ba tare da gurfanar da shi a kotu ba, wanda hakan haramun ne a doka.

Kara karanta wannan

Okupe: Tsohon hadimin shugaban ƙasa ya fice daga jam'iyyarsa, ya bayyana muhimmin dalili

Kotu ta ci tarar FG da EFCC

Alkalin ya ci tarar FG da EFCC Naira miliyan 100 (wadanda ake ƙara na ɗaya da na biyu), kuma za a bai wa mai kara waɗannan kuɗaɗe saboda tauye masa haƙƙi.

Ya kuma bada umarnin hana wadanda ake karan su ƙara kama Emefiele tare da tsare shi ba tare da samun umarni hakan daga kotun da ta dace ba, Channels tv ta ruwaito.

Doyin Okupe ya fice daga Labour Party

A wani rahoton Mista Doyin Okupe, tsohon kakakin shugaban ƙasa sau biyu, ya fice daga jam'iyyar LP ranar Litinin, 8 ga watan Janairu, 2024.

Tsohon darakta janar na kwamitin yaƙin neman zaben Peter Obi ya ce ba zai iya ci gaba da zama a LP ba bayan sun sha kaye a 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel