Yayin da Ta Ke Binciken Wasu, EFCC Ma Ta Ware Wa Kanta N1bn Don Tafiye-Tafiye da N413m Kan Motoci
- A yayin da hukumar EFCC ke binciken wasu kan kudaden da suka kashe, ita ma hukumar ta ware biliyoyi da za ta kashe a 2023
- Daga cikin manyan kudaden da za ta kashe akwai naira biliyan 1,055,633 na tafiye-tafiye, da naira miliyan 413 na sayen motoci
- Ba a nan ta tsaya ba, EFCC ta ce za ta kashe naira miliyan 71.3 wajen sayen abinci da kayan makulashe don karfafa guiwar ma'aikata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arziki zagon kasa a Najeriya (EFCC) za ta kashe naira biliyan 1,055,633,61 akan tafiye-tafiye, kamar yadda kasafin 2024 ya nuna.
Haka zalika hukumar za ta kashe naira miliyan 113.4 wajen horas da ma'aikatanta, yayin da ta ware naira miliyan 563.2 don tafiye-tafiye zuwa kasashen waje da kuma karo ilimi ga ma'aikata.
K ari kan hakan, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, hukumar za ta kashe naira miliyan 413 wajen sayen motoci da kuma naira miliyan 164.3 don shan man motocin hukumar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kudaden da EFCC za ta kashe a Abinci, buga takardu da sauran su
Hukumar ta kuma ware naira miliyan 273.3 don zuba mai a janareto da kuma naira miliyan 156.8 don biyan kudin wutar lantarki.
Rahoton ya kuma nuna cewa hukumar za ta kashe naira miliyan 71.3 na sayen abinci, da kuma naira miliyan 413.7 don sayan kayan ofis, da naira miliyan 352.1 na kula da ofisoshin.
Duk da hakan, hukumar ta ce tana da bukatar kashe basira miliyan 65.2 don buga takardu na tsaro, da naira miliyan 46 na buga takardun da ba na tsaro ba, rahoton The Cable.
Jerin Hukumomin Gwamnati Da Suka Bada Kyauta Ga Matar Da Ke Tashi 4.50 Na Asuba Don Yi Wa Mijinta Girki
Akwai kuma naira miliyan 455 da hukumar EFCC ta ware don inshorar lafiyar ma'aikatanta da kuma naira miliyan 44.1 na kula da kasafin hukumar da gudanarwar ta.
Tsohuwar ministar Buhari, Sadiya ta mika kanta ga hukumar EFCC
A safiyar yau ne muka kawo maku rahoton cewa tsohuwar ministar jin kai a zamanin Buhari, Hajiya Sadiya Umar-Farouq, ta mika kanta ga hukumar EFCC a Abuja.
Hakan na zuwa ne bayan da EFCC ta nemi Sadiya ta bayyana gabanta don amsa wasu tambayoyi da suka shafi zargin ta karkatar da kudi sama da naira biliyan 37.
Asali: Legit.ng