Innalillahi: Mutum 1 Ya Rasa Ransa Bayan Mummunar Gobara Ta Lakume Gidan Mai a Kano

Innalillahi: Mutum 1 Ya Rasa Ransa Bayan Mummunar Gobara Ta Lakume Gidan Mai a Kano

  • Mummunan gobara ta yi ajalin wani mutum daya a gidan mai da ke jihar Kano a yau Litinin 8 ga watan Janairu
  • Gobarar ta kama ne a ma'ajiyar bakin mai da ke yankin Hotoro inda ta yi sanadin asarar dukiyoyi a kamfanin
  • Hukumar kashe gobara a jihar ta yi hanzarin kawo daukin gaggawa inda ta dakile gobarar a Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Mutum daya ya rasa ransa yayin da gobara ta cinye ma'ajiyar bakin mai a Kano.

Gine-gine da dama da ke cikin ma'ajiyar sun kone a mummunar gobarar a yankin Hotoro sa ke bayan gari.

Gobara a gidan mai ta lakume ran wani mutum 1 a Kano
Mutum 1 Ya Rasa Ransa Bayan Mummunar Gobara Ta Lakume Gidan Mai a Kano. Hoto: Abba Kabir Yusuf.
Asali: Twitter

Wane mataki hukumar kashe gobara ta yi?

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kashe basarake da wani manomi, sun tafka mummunar ɓarna a jihohin arewa 2

Hukumar kashe gobara a jihar ta kawo daukin gaggawa bayan shafe awanni uku inda ta dakile gobarar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mutane da dama da ke kusa da inda abin ya faru sun tsare daga wurin da don tsira da rayuwarsu.

Shaidan gani da ido ya tabbatar wa Daily Trust cewa wutar ta kama ne bayan wata tanka makare da mai ta zo harabar kamfanin.

Wace asara gobarar ta jawo a Kano?

Har zuwa lokacin tattara wannan rahoto ba a iya kayyade yawan asara da aka tafka ba yayin gobarar.

Rahotanni sun tabbatar da cewa ma'ajiyar mai din an kirkire ta ce ba bisa ka'ida ba inda gobarar ta tashi, cewar Platinum Post.

Wanda ake tunanin ya rasa ransa a gobarar sunansa Aminu yayin da ya kone kurmus yadda ba za a gane shi ba.

Wata majiya ta ce gidajen da ke kusa inda gobarar ta kama duk sun kone sanadin mummunar gobarar da ta kama.

Kara karanta wannan

Tinubu ya umarci a yi bincike kan kudin tallafin talakawa N37bn da aka sace a ofishin Betta Edu

Gobara ta lakume kasuwa a jihar Arewa

A wani labarin, mummunar gobara ta yi sanadin asarar dukiyoyi a babbar kasuwar Oja Tuntun da ke birnin Ilorin a jihar Kwara.

Rahotanni sun tabbatar cewa gobarar ta tashi ne da misalin karfe 10 na daren ranar Laraba 22 ga watan Nuwamba.

Akalla gobarar ta lakume shaguna fiye da 15 inda aka tabbatar cewa kasuwar na dauke da shaguna fiye da dubu daya a cikinta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.