Ana Tsaka da Tsadar Mai a Najeriya, Tinubu Ya Tura Muhimmin Sako Ga Shugaban NNPCL, Kyari

Ana Tsaka da Tsadar Mai a Najeriya, Tinubu Ya Tura Muhimmin Sako Ga Shugaban NNPCL, Kyari

  • A yayin da ake ke tsaka da tsadar man fetur a Najeriya, Shugaba Tinubu ya tura wa shugaban NNPC sako a ranar Litinin
  • A sakon da ya tura wa Malam Mele Kyari ta hannun Chief Ajuri Ngelale, shugaban kasar ya taya Kyari murnar cika shekara 59
  • Shugaba Tinubu ya gwarzanta Mele Kyari inda ya kira sa da Mahadi mai dogon zamani a shugabancin kamfanin NNPC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Tinubu ya aike da muhimmin sako ga Malam Mele Kyari, shugaban kamfanin man fetur na Najeriya (NNPCL).

Bola Tinubu ya aike da sakon taya murnar zagayowar ranar haihuwar Kyari, wanda ya cika shekaru 59 da haihuwa a yau Litinin.

Kara karanta wannan

"Ba zama": Gwamnan jihar Arewa ya yi ganawar sirri da Shugaba Tinubu a Abuja, an gano dalili

Tinubu ya taya Mele Kyari murnar zagayowar ranar haihuwarsa
Tinubu ya yi biris da tsadar mai, ya jinjinawa shugaban NNPCL, Mele Kyari a ranar haihuwarsa
Asali: Twitter

Shugaban kasar ya ayyana Kyari matsayin hazikin mutum wanda kokari da jajurcewarsa ta saka ya rike mukamin shugabancin kamfanin na tsawon lokaci da ba a taba rike wa ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mele Kyari ya san sirrin warware duk wata matsala ta NNPCL - Tinubu

Cikin wata sanarwa da fadar gwamnatin Najeriya ta fitar a Twitter, dauke da sa hannun Chief Ajuri Ngelale, Tinubu ya ce:

"Mele mutum ne mai fada a cika, kuma shi kaifi daya ne kan duk abin da ya saka a gaban sa. Samar da hanyoyin warware matsala a duk sanda ta taso ya sa shi zama Mahadi mai dogon zamani."

Shugaba Tinubu sai ya yi addu'ar Allah ya kara wa Mele Kyari basirar tafiyar da aikinsa, da kuma hidimtawar da ya ke yi wa Najeriya, Leadership ta ruwaito.

Tinubu ya gwarzanta gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf

Kara karanta wannan

Don burge Bankin Duniya: An tona asirin dalilin Tinubu na kara farashin mai da wutar lantarki

A wani labarin makamancin wannan, shugaba kasa Tinubu ya aika wa gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf wata muhimmiyar wasika a zagayowar ranar haihuwarsa.

A ranar Alhamis din da ta gabata, Tinubu ya taya Abba Gida-gida murnar cika shekara 61 a duniya, tare da kiran sa "jan gwarzo".

Tunubu ya yabi Gwamna Abba ana tsaka da jiran sakamakon da Kotun Koli za ta yanke kan shari'ar gwamnan Kano, wanda ake sa ran za a kai karshe ranar Juma'a mai zuwa.

Kano: Dan Majalisa ya raba miliyoyin naira ga dalibai 512 a mazabarsa

Har ila yau daga jihar Kano, dan majalisar da ke wakilartar mazabar Fagge a majalisar tarayya, Mohammed Bello, ya raba wa dalibai 512 na mazabarsa naira miliyan 50.

A cewar Mohammed Bello, tallafin zai taimaka wa daliban su biya kudin makarantar su, da suka hada da daliban jami'a da na sakandire.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.