'Yan Bindiga Sun Kashe Basarake da Wani Manomi, Sun Tafka Mummunar Ɓarna a Jihohin Arewa 2
- Yan bindiga sun kai hari jihohin Taraba da Kaduna, sun kashe basarake da wani manoni, sannan sun sace mutane da dama
- Bayanai sun nuna maharan sun kashe Magajin Garin ƙauyen Wuro Musa a Taraba kwanaki kaɗan bayan sun yi garkuwa da shi
- Mahara sun mamaye kauyukan Dinki da Kidandan a Kaduna, inda suka kashe mutum ɗaya da daren ranar Asabar
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Wasu tsagerun ‘yan bindiga sun kashe Magajin Garin kauyen Wuro Musa, Jauro Kabiru Gambo, a karamar hukumar Yorro a jihar Taraba.
Tun farko dai an yi garkuwa da basaraken ne tare da wasu mutane 17 da suka hada da mata bakwai lokacin da ‘yan bindiga suka kai farmaki kauyen ranar Juma’a.
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa an tsinto gawar marigayin a cikin dajin da ke kusa da wani dutse a yankin da sanyin safiyar Lahadi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sani Adamu, majiya daga yankin, ya ce an yi jana’izar marigayi Jauro Gambo tare da binne shi a makabartar Jaka Da Fari da ke Jalingo da misalin karfe 3 na yammacin Lahadi.
Mutumin ya ce sauran mutane 16 suna hannun ƴan bindigan har kawo yanzu yayin da suka nemi fansar Naira miliyan ɗaya kan kowane mutum daya daga ciki.
Wannan lamari ya sa adadin sarakunan da ‘yan bindiga suka kashe a jihar zuwa hudu yayin da wasu ‘yan bindiga suka kashe ‘yan uwa bakwai na sarkin Mutumbiyu a bara.
Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Taraba, SP Usman Abdullahi, ya tabbatar da kisan basaraken kauyen, kamar yadda Dailypost ta rahoto.
Ƴan bindiga sun kashe manomi a Kaduna
‘Yan bindiga sun kashe wani manomi tare da yin garkuwa da wasu mutane 22 a kauyukan Dinki da Kidandan da ke kananan hukumomin Igabi da Giwa a jihar Kaduna.
Jafaru Anaba, wani shugaban al’umma da ke kusa da kauyen Dinki ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce wasu mutanen kauyen sun bace.
Anaba ya ce:
"Bamu san meke faruwa ba yanzu haka saboda ƴan bindiga sun mamaye mu, sun kashe mutum ɗaya tare da sace wasu 16 ranar Asabar da daddare a kauyen Dinki, kuma ba matakin da aka ɗauka."
Har kawo yanzu dai babu wata sanarwa a hukumance daga rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna.
DHQ ta faɗi nasarorin sojoji a mako ɗaya
A wani rahoton kuma Dakarun sojojin Najeriya sun yi nasarar sheƙe yan ta'adda 43 tare da kamo wasu sama da 100 a samame daban-daban cikin mako ɗaya
Hedikwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) ta ce yanzu sojoji suna bin yan bindiga har cikin dajin da suke ɓuya, su halaka su.
Asali: Legit.ng