Gwamna Uba Sani Ya Yi Allah Wadai da Hare-Haren Yan Bindiga, Ya Sha Muhimmin Alwashi

Gwamna Uba Sani Ya Yi Allah Wadai da Hare-Haren Yan Bindiga, Ya Sha Muhimmin Alwashi

  • Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna ya yi Allaj wadai da sabbin hare-haren da ƴan bindiga suka kai wasu ƙananan hukumomin jihar
  • A haren-haren da ƴan bindigan suka kai sun halaka mutum 15 tare da raunata wasu mutum 38
  • Gwamnan ya bayyana ƴan bindigan a matsayin dabbobi cikin fatar ɗan Adam inda ya sha alwashin farauto su domin su fuskanci hukunci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya yi Allah-wadai da hare-haren da ƴan bindiga suka kai wasu ƙauyuka a ƙananan hukumomin Kauru da Kajuru na jihar.

Sama da mutum 15 aka ruwaito an kashe tare da sace wasu mutum 38 yayin hare-haren da ƴan bindigan suka kai.

Kara karanta wannan

Asiri ya fara tonuwa: An kama mutum 8 da ake zargi da hannu a kisan bayin Allah sama da 150

Uba Sani ya yi Allah wadai da hare-haren yan bindiga
Gwamna Uba Sani ya sha alwashin ragargazar yan bindiga Hoto: @ubasanius
Asali: Twitter

Gwamnan na Kaduna a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a, ya bayyana waɗanda suka kai hare-haren a matsayin “dabbobi a fatar mutum”.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce waɗanda suka aikata wannan aika-aika ba su da wani matsayi a cikin al’umma, domin haka gwamnatin jihar za ta yi duk mai yiwuwa wajen ganin ta farauto su domin a hukunta su.

Gwamna Sani ya yi Allah wadai da harin

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"Mun samu labari daga jami’an tsaro cewa wasu ƴan bindiga sun kai hari a yankin Dokan Karji a ƙaramar hukumar Kauru da wasu wurare a yankin Gefe a ƙaramar hukumar Kajuru.
"A waɗannan wurare, an yi asarar rayuka, an yi garkuwa da wasu mutane, wasu kuma sun jikkata a hare-haren marasa daɗi."

Wane alwashi gwamnan ya ɗauka?

Sanarwar ta cigaba da cewa:

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun yi garkuwa da mutum 7 yan gida ɗaya, sun tafka mummunar ɓarna a Abuja

"Muna yin Allah wadai da waɗannan ayyukan ta’addanci. Masu aikata waɗannan munanan laifuka ba su da gurbi a cikin al’umma mai wayewa irin tamu. Za mu bi duk wata hanya domin farauto su, mu gurfanar da su a gaban kotu
"Manufar waɗannan namomin jeji a fatar ɗan Adam kawai shine su kawo koma baya kan irin nasarorin da mutanen jihar Kaduna suka samu na sake gina amana da fahimtar juna da farfaɗo da tattalin arzikin ƙauyukan da ke fama da rikici."

Gwamnan ya kuma miƙa saƙon ta'aziyyarsa gaa iyalan waɗanda suka rasa ransu, tare da yin addu'ar samun sauƙi ga waɗanda suka jikkata a hare-haren.

Ƴan Sanda Sun Daƙile Harin Ƴan Bindiga

A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ta sanar da cewa ta daƙile yunƙurin sace wani magidanci da matarsa a Kaduna.

Rundunar ta daƙile yunƙurin ƴan bindigan ne a yankin Rigasa na ƙaramar hukumar Igabi ta jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng