Matashi Ya Ba Budurwarsa Ta Shekaru 7 Naira Miliyan 5 Don Ta Bari Ya Auri Wata Daban, Ta Yi Martani
- Wata matashiya yar Najeriya da ta shafe shekaru bakwai tana soyayya da wani mutum ta samu karayar zuciya bayan ya gabatar mata da wata bukata mai ban mamaki
- Masoyin nata ya samu wata sabuwar mace da yake son yin rayuwa da ita, sai ya yi mata tayin naira miliyan 5 domin ta rabu da shi
- Masu amfani da soshiyal midiya sun bayyana ra'ayoyinsu, inda da dama suka shawarceta da ta karbi kudin
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Soyayyar wata matashiyar budurwa yar Najeriya da sahibinta na shekaru bakwai ta hadu da tangarda.
A cewar wata mai amfani da dandalin X @dexterouz11, sahibinta ya hadu da wata sabuwar masoyiya don haka ya nemi su raba gari da ita.
Matashi ya yi wa budurwa tayin naira miliyan 5 do ta rabu da shi
A cewarta, ya mata alkawarin makudan kudade har naira miliyan 5 idan har ta rabu da shi duk da kasancewar sun shafe tsawon lokaci tare.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai kuma, matashiyar wacce ta karaya sosai, tare da jin radadi sosai a zuciyarta fiye da tsammani, tana duba yiwuwar rabuwa da shi ba tare da ta karbi kudinsa ba.
@dexterouz11 ta rubuta:
"Wata kawata ta shafe shekaru 7 tana soyayya da wannan gayen kuma yanzu ya samu wata daban sannan ya yi mata tayin naira miliyan 5 don ta rabu da shi. Tana duba yiwuwar rabuwa da shi ba tare da ta karbi ko sisi daga hannusa ba."
Jama'a sun yi martani
@julienwakanma ta ce:
"Zan karbi kudin a kalla na lokacin da na bata rayuwarsa ba za ta tafi daidai ba."
@Kajnyee ta ce:
"Ban ga laifinta ba a kan wannan. Abun bakin ciki ne sosai."
@sarahadamm ta ce:
"Allah ya tsine masa da kudinsa."
@anna66 ta yi martani:
"Karbi kudinki yar'uwa. Kudi ya yi wuya."
@jerey7 ta kara da cewar:
"Na turo lambar asusuna?"
Ga wallafar a kasa:
Tsegumi ya kai matasa ya baro
A wani labari na daban, mun ji cewa rundunar yan sandan Najeriya mai yaki da laifuka ta Intanet, ta kama wasu mutane uku da ake zargi da hada kai da kuma barazana ga rayuwar wata, sakamakon korafin da wata mata mai suna Misis Seye Oladejo ta yi.
Wata sanarwa da kakakin rundunar yan sandan Najeriya, ACP Olumuyiwa Adejobi, ya fitar ta tabbatar da cafke Adebukola Kolapo mai shekaru 27, Nnedum Micheal Somtomchukwu mai shekaru 25 da Isaac Akpokighe mai shekaru 30.
Asali: Legit.ng