Dakarun Sojojin Sun Sheke Yan Ta'adda 10, Sun Ceto Mutanen da Suka Sace

Dakarun Sojojin Sun Sheke Yan Ta'adda 10, Sun Ceto Mutanen da Suka Sace

  • Dakarun sojoji na Operation Hadarin Daji sun samu gagarumar nasara kan miyagun ƴan ta'adda a jihohin Zamfara da Katsina
  • Dakarun sojojin a yayin wani farmaki da suka kai a jihar Katsina, sun samu nasarar salwantar da ran ƴan ta'adda 10
  • A jihar Zamfara kuwa sojojin sun ceto mutanen da ƴan ta'addan suka sace bayan sun yi wani artabu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Katsina - Dakarun sojojin Najeriya sun kashe ƴan ta'adda 10 tare da kuɓutar da wasu mutum tara da aka yi garkuwa da su a wani farmaki a jihohin Zamfara da Katsina.

Sojojin da ke ƙarƙashin jagorancin babban kwamandan runduna ta takwas ta sojojin Najeriya, Manjo Janar Godwin Mutkut, sun kuma ƙwato makamai da alburusai da suka haɗa da babura da na'urorin sadarwa.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun shiga har fada sun yi awon gaba da babban basarake

Sojoji sun halaka yan ta'adda
Dakarun sojoji sun halaka yan ta'adda 10 a Katsina Hoto: Nigerian Army
Asali: Twitter

Yayin da aka kashe ƴan ta’addan guda 10 a Katsina, waɗanda aka sace da suka haɗa da mata huɗu da jarirai biyar an kuɓutar da su a dazuzzukan Zamfara, cewar rahoton PM News.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sojoji sun samu nasara kan ƴan ta'adda

Jaridar Nigerian Tribune ta ce da yake bayar da cikakken bayani kan ayyukan rundunar a wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis ya bayyana cewa:

"Musamman a ranar 3 ga watan Janairun 2024, rundunar hadin gwiwa ta OPHD ta kai wani samame a yankunan Batsari da Safana na jihar Katsina, inda suka kashe ƴan ta'adda 10, yayin da sauran suka gudu da raunukan harbin bindiga.

"Sojojin sun kuma ƙwato bindiga ƙirar AK-47 guda ɗaya, alburusai, ƙananan bindigogi guda bakwai, bindigu na gida guda uku, da sauran muggan makamai da na’urorin sadarwa, wayoyin hannu da kakin soja yayin da aka ƙwato tare da lalata babura huɗu a wurin."

Kara karanta wannan

DHQ: Dakarun Sojojin Najeriya sun halaka 'yan bindiga sama da 40, sun samu gagarumar nasara

Sojoji sun ceto mutanen da aka sace

Sanarwar ta cigaba da cewa:

"Hakazalika, a wannan rana, sojojin na Operation Hadarin Daji da ke aiki a jihar Zamfara, sun gudanar da aikin bincike da ceto a ƙauyukan Dansadau da Dandalla dake ƙaramar hukumar Maru ta jihar Zamfara.
"A yayin aikin, an ceto mutum tara da aka yi garkuwa da su wadanda suka hada da, mata biyar da jarirai huɗu.
"Ƴan ta’addan sun gudu ne sun bar mutanen da suka sace bayan sun yi artabu da dakarun sojoji. Nan da aka haɗa mutanen da aka ceton da iyalansu a ƙauyen Magami."

Legit Hausa ta samu jin ta bakin wani mazaunin jihar Katsina, mai suna Malam Sahabi wanda ya yaba da wannan namijin ƙoƙarin da dakarun sojojin suka yi.

Sahabi ya bayyana cewa abin da sojojin suka yi ya cancanci yabo, inda ya ƙara da addu'ar Allah ya ƙara musu ƙarfin gwiwa wajen cigaba da fatattakar miyagu a jihar Katsina.

Kara karanta wannan

Asiri ya fara tonuwa: An kama mutum 8 da ake zargi da hannu a kisan bayin Allah sama da 150

Ya bayyana cewa an samu cigaba sosai a fannin tsaro a jihar, tun bayan da jami'an tsaro suka ƙara ƙaimi wajen fatattakar ƴan ta'adda.

Sojoji Sun Halaka Ƴan Bindiga Sama da 40

A wani labarin kuma, kun ji cewa hedikwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) ta bayyana cewa dakarun sojoji sun samu nasarar sheƙe ƴan bindiga sama da 40 cikin mako guda.

Dakarun sojojin sun sheƙe ƴan ta'addan ne a cigaba da ƙoƙarin da suke na kawo ƙarshen matsalar tsaro a ƙasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng