Ministar Tinubu Ta Bayyana Rawar da Ta Taka a Badakalar Almundahanar N3bn Daga Hukumar NSIPA

Ministar Tinubu Ta Bayyana Rawar da Ta Taka a Badakalar Almundahanar N3bn Daga Hukumar NSIPA

  • Ministar harkokin jin kai da yaƙi da fatara, Dr Betta Edu, ta mayar da martani kan badaƙalar cin hanci da rashawa ta N3bn a hukumar NSIPA
  • Edu ta musanta zargin da ake mata na hannu a badaƙalar cin hancin Naira biliyan 3, inda ta bayyana hakan a matsayin aikin masu yaɗa jita-jita
  • Ministar ta ce ba ta taɓa neman Naira biliyan 3 ba daga hukumar NSIPA tun bayan da ta zama minista

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ministar harkokin jin ƙai da yaƙi da fatara, Dr Betta Edu, ta ce ba ta da alaƙa da almundahanar Naira biliyan 3 da aka yi a hukumar jindaɗin al'umma ta ƙasa (NSIPA).

Kara karanta wannan

"Gwanin sha'awa" Hotunan yadda wata gabjejiyar budurwa ta rage ƙiba ta zama yar cas-cas sun girgiza Intanet

Edu ta bayyana sanya ta a cikin almundahanar N30bn a matsayin ƙarya wacce kuma ba ta da tushe ballantana makama.

Edu ta yi magana kan zargin cin hancin N3bn
Betta Edu ta musanta hannu a badakalar N3bn Hoto: @edu_betta
Asali: Twitter

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Legit.ng ta samu mai taken “Betta Edu na da alaƙa da badakalar zamba ta N3bn a NSIPA; zarge-zarge marasa tushe da nufin karkatar da hankalin hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane martani ministar tayi?

Ministar ta ce ƴan jarida masu yaɗa jita-jita da ke da niyyar ɓata mata suna da mutuncin ta ne ke da alhakin wannan zargi.

Edu ta ce ba ta nema ko ba da izinin cire Naira biliyan 3 daga asusun hukumar NSIPA ba tun da ta hau muƙamin minista.

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"Domin tabbatarwa, duk shirye-shiryen da ma'aikatar ta fara a ƙarƙashin minista ta yanzu, Dakta Betta Edu, ya zuwa yanzu, ciki har da Enterprise Government and Empowerment Programme (GEEP), Grant for Vulnerable Groups (GVG) da sauran su sun sami amincewar mai girma shugaban ƙasa."

Kara karanta wannan

Hukumar EFCC za ta yi wa Sadiya Farouk tambayoyi kan zargin karkatar da N37bn a gwamnatin Buhari

"Haka kuma, a sani cewa babu wani lokaci da ma’aikatar ta cire kuɗi daga asusun NSIPA, balle Naira biliyan 3 ba tare da bin ƙa'ida ba, da kuma samun amincewar hukumomin da suka dace."

Tinubu Ya Dakatar da Shugabar NSIPA

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya dakatar da shugabar hukumar jindaɗin al'umma ta ƙasa, Halima Shehu.

Shugaban ƙasan ya kuma bayar da umarnin a gudanar da cikakken bincike kan yadda ta tafiyar da hukumar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng