An Tara wa Matar Aure Naira Miliyan Daya Cikin Awanni Sanadin Tashi da Asuba Ta Yi Wa Mijinta Girki

An Tara wa Matar Aure Naira Miliyan Daya Cikin Awanni Sanadin Tashi da Asuba Ta Yi Wa Mijinta Girki

  • Wata matashiya yar Najeriya ta sha jinjina a soshiyal midiya kan cewa tana tashi da karfe 4:50 na asuba domin girkawa mijinta abinci
  • Bayan an caccaketa a dandalin X saboda furucin da ta yi, maza sun tara tare da aika mata kudi sama da naira miliyan 1
  • Matashiyar da ta cika da farin ciki ta baje kolin kudin asusunta yayin da ta bayyana wani karin abun da wani ya yi mata duk a kan lamarin

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jim kadan bayan mata da dama sun caccaketa a soshiyal midiya, wata matar aure mai suna @_Debbie_OA, ta samu kyautar sama da naira miliyan 1 daga wajen mutane.

Kara karanta wannan

"Sun kama kansu": Matashi ya yi arba da yan mata 18 da suka yi soyayya a wajen bikinsa

@_Debbie_OA ta shahara ne bayan ta bayyana yadda take tashi da karfe 4:50 na asuba domin girkawa mijinta abinci bayan ya fada mata cewar abokiyar aikinsa ta kawo cokula biyu don su ci abinci tare.

Matashiya ta samu kyautar kudi saboda girkawa mijinta abinci
An tara wa matar aure naira miliyan daya cikin awanni sanadin tashi da asuba ta yi wa mijinta girki Hoto: @_Debbie_OA
Asali: Twitter
"Na kasance mai kiwiyar tashi na shirya masa abinci. Amma a ranar da ya fada mani cewa wani abokinsa ya kawo cokula biyu don ya ci abinci tare da ita, daga sannan ne na yi saitin agogona kan karfe 4:50 na asuba," ta rubuta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wani rubutu da ya biyo baya, ta baje kolin kudin da ke asusunta wanda ke nuna sama da naira miliyan 1 da ta samu sannan ta yi godiya ga dukkanin wadanda suka bayar da gudunmawa. Ta rubuta:

"Ga duk wanda ke da hannu a wannan, ba ni da kalaman furtawa, amma na cika zuciyata da addu'o'i ga duk wanda ya ba da gudunmawa, ya yada da kuma yi mani fatan alkhairi. Kaina na radadi kuma yanzu nake son tashi.

Kara karanta wannan

Kaza mafi tsufa a duniya ta mutu cikin baccinta tana da shekaru 21 a duniya a ranar Kirsimeti

"Ina godiya gareku ku dukka."

Ta kuma kara da cewa wani ya ba da shawarar a bata tallafi tare da biyanta N50k duk wata.

Kalli wallafarta a kasa:

Jama'a sun yi martani

@ill_nojie ta ce:

"Yanzu ba sai kin dunga tashi karfe 4:30 ba kullun. Kina iya girkawa yanzu sannan ki saka a katon firinjin da za ki siya."

@mister_ade5 ya ce:

"Idan ba ki zama mutuniyar kirki ba, walai yunwa ce za ta gama da ke a wannan 2024 din.
"Mun mika matan auren da ba nagari ba a hannun Tinubu."

@Alan_yournextbf ya ce:

"Wannan shekarar 2024 din na skawa mata nagari ne, babu wannan aikin turawa mata kudi don su amsa maka sakonsa ko kuma don kawai suna da katon mazauni."

Matashiya ta koka kan saurayi

A wani labarin, mun ji cewa wata matashiya ta koka a soshiyal midiya bayan da saurayinta ya yi watsi da ita a filin jirgin sama.

A cikin wani bidiyo da ya samu mutum fiye da miliyan hudu a TikTok, @datgirl_dime ta ce ya ki zuwa ya dauke ta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng