Karfin hali: Ya lakadawa mai gida duka saboda zata fitar da shi daga gidan haya

Karfin hali: Ya lakadawa mai gida duka saboda zata fitar da shi daga gidan haya

- Wani dan haya ya nakadawa wa mai gida dukka saboda ta kayyade masa kwanakin barin mata gidanta

- Fadan ya kaure ne bayan mai gidan, Mrs Omiwunmi Omoroga ta tambaye shi ranar da zai bar mata gidan ta

- Sai dai dan hayan ya musanta cewa ya doke ta yayin daya gurfana gaban Alkali

Kabiru Tajudden dan shekara 30 wanda ya daki me gidan da yake haya akan ta bashi notice ya bayyana a gaban kotun majistire dake Okeja. Tajudden wanda yake zaune a gida me lamba 28 Omoroga street, powerline, Meiran wata unguwa a gefen Lagas yayi kokarin kai farmaki.

Wani 'dan haya ya daki mai gidan akan ta kayyade masa kwanakin barin mata gida
Wani 'dan haya ya daki mai gidan akan ta kayyade masa kwanakin barin mata gida

Inspector Raji Akeem ya bayyanawa kotu cewa Tajudden ya aikata laifin ne a ranar 1 ga watan afrilu a gidan da yake zaune. Akeem yace me gidan Mrs Omiwunmi Omoroga ta bashi notice a dalilin zargi tun a 2017 amma yaki.

KU KARANTA: Abubuwa 10 da ya kamata ka sani game da Sanata Ovie Omo-Agege

Fadan ya farane a lokacin da me gidan ta tambayashi yaushe zai tashi. Wanda ake zargin ya daki mai kai karar wanda nan da nan wasu masu sufiri sukai asibiti da ita. Yace laifin ya sabawa doka ta 173 na jahar legas 2015 a bangaren Akeem kenan.

Tajudden ya musanta aikata laifin da ake tuhumarsa dashi.

Shugaban majistire, Jadesola Adeyemi Ajayi ta bayar belin sa akan kudi N50,000 tare da tsaidu biyu. Adeyemi Ajayi ta dage sauraran karar har zuwa 7 ga watan mayu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel