Ka Tsamo 'Yan Kano Daga Mummunan Mulkin APC, Jigon NNPP Ya Kora Yabo Ga Abba Kabir

Ka Tsamo 'Yan Kano Daga Mummunan Mulkin APC, Jigon NNPP Ya Kora Yabo Ga Abba Kabir

  • Gwamna Abba Kabir ya na shan yabo a wurin mutanen Najeriya bayan murnar cika shekaru 61 a duniya
  • Jigon jam'iyyar NNPP, Olufemi Ajadi ya bayyana gwamnan a matsayin wanda ya ceci al'ummar jihar daga kangin talauci a mulkin APC
  • Ajadi ya bayyana gwamnan a matsayin shugaba wanda ba za a iya kwatanta irin ci gaban da ya kawo ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Jigon jam'iyyar NNPP, Olufemi Ajadi ya taya Gwamna Abba Kabir na jihar Kano murnar cika shekaru 61 a duniya.

Ajadi ya bayyana gwamnan a matsayin shugaba wanda ba za a iya kwatanta irin ci gaban da ya kawo ba.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa ya fadi babban burin Tinubu kan talakawan Najeriya, ya roki 'yan kasar kan hakuri

Jigon NNPP ya bayyana kokarin da Abba Kabir ya yi a Kano
Abba Kabir ya sha yabo daga jigon jam'iyyar NNPP. Hoto: Abba Kabir Yusuf.
Asali: Facebook

Mene Ajadi ya ce kan Abba Kabir?

Olufemi ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa a yau Juma'a 5 ga watan Janairu, cewar Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce jama'ar jihar Kano sun yi sa'ar samun gwamnan mai tsoron Allah da aiki tukuru wanda ya zamo haske a gare su.

Ya kara da cewa gwamnan ya zama jakadan jamiyyar kuma wanda ya nuna wa jama'ar Najeriya cewa NNPP ba ta zo da wasa ba.

Wane yabo ya yi kan mulkin Abba Kabir?

A cewarsa:

"Ka nuna wa 'yan Najeriya cewa jam'iyyar NNPP ta na da burin kyautatawa mutane, yanzu ka zama jakadan jamiyyar NNPP a fadin kasar baki daya.
"Mutanen Kano sun sha romon dimukradiyya da tsare-tsaren jami'yyar mu wanda ka bi shi daki-daki don tsamo su daga mulkin kama-karya.

Ajadi ya ce tabbas 'yan jihar sun fita daga mulkin kama-karya daga gwamnatin da ta shige ta jami'yyar APC a jihar, cewar Blueprint.

Kara karanta wannan

Gwamna Fubara ya bayyana dalili 1 da yasa ya amince da yin sulhu a rikicinsa da Wike

Olufemi wanda ya yi takarar gwamna a jam'iyyar a jihar Ogun ya ce Abba Kabir ya gagari 'yan adawa wurin neman bata masa suna.

Tinubu ya yabi Gwamna Abba Kabir

A wani labarin, Shugaban kasa, Bola Tinubu ya taya Gwamna Abba Kabir Yusuf murnar cika shekaru 61 a duniya.

Tinubu ya bayyana haka ne a jiya Alhamis 4 ga watan Janairu inda ya ce tabbas gwamnan ya yi namijin kokari wurin ayyukan alkairi.

Wannan na zuwa ne yayin da ake dakon hukuncin Kotun Koli bayan kotun ta tanadi hukunci a kwanakin baya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.