An Cafke Babban Kwamandan Sojoji Bisa Hannu Kan Hare-Haren Plateau? Gaskiya Ta Bayyana

An Cafke Babban Kwamandan Sojoji Bisa Hannu Kan Hare-Haren Plateau? Gaskiya Ta Bayyana

  • Runduanr tsaro ta Operation Safe Haven (OPSH) ta yi ƙarin haske kan rahotannin dake yawo dangane da cafke kwamandanta
  • Rundunar ta bayyana rahotannin a matsayin na ƙarya waɗanda aka ƙirƙire su domin ɓata sunan dakarun rundunar
  • Kakakin OPSH a wata sanarwa da ya fitar ya yi kira ga jama'a da su yi watsi da rahotannin domin babu ƙamshin gaskiya a cikinsu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Plateau - Rundunar tsaro ta Operation Safe Haven (OPSH) reshen jihar Plateau ta musanta zargin da ake na cewa ta cafke kwamandanta da ke ƙaramar hukumar Bokkos.

An yaɗa cewa an cafke kwamandan ne sakamakon wani mummunan lamari da ya yi sanadin mutuwar sama da mutum 100 a yankin.

Kara karanta wannan

Gwamnonin Arewa ta Tsakiya sun fadi abu 1 da FG za ta yi ka hare-haren Plateau

Rundunar OPSH ta musanta cafke kwamandanta
Rundunar OPSH ta musanta cafke kwamandanta kan hare-haren Plateau Hoto: Nigerian Army
Asali: Twitter

Wasu rahotanni sun yaɗu cewa an kama kwamandan sashi na biyar na rundunar ne bisa zargin hannu a hare-haren da aka kai a ƙananan hukumomin Bokkos, Barkin Ladi da Mangu na jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai, a martanin da rundunar ta yi, ta bayyana rahoton a matsayin ƙarya da yaudara, cewar rahoton The Punch.

Wane martani rundunar OPSH ta yi?

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da Kaftin Oya James, mai magana da yawun rundunar ya fitar a birnin Jos.

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"Rahoton ba wai kawai ba shi da tushe ba balle makama, amma wani yunƙuri ne na ɓata sunan dakarun sojojin mu da kuma ɓata ƙoƙarin Operation Safe Haven na tabbatar da masu laifin sun fuskanci hukunci."
"Rundunar OPSH na kira ga jama'a, ɗaidaikun mutane, ƙungiyoyi da duk masu ruwa da tsaki da su marawa dakarunmu baya ta hanyar bayar da sahihan bayanai da za su taimaka wajen ƙoƙarin da ake na dawo da zaman lafiya a yankin.

Kara karanta wannan

Cikakken jerin jami'o'in kasashen waje da gwamnatin Tinubu ta haramta a Najeriya

“Muna kira ga jama’a da su yi watsi da labaran ƙarya da ake yaɗawa, domin an tsara su ne domin biyan buƙatun masu son kai waɗanda ke yaɗa su."

Gwamnonin Arewa Ta Tsakiya Sun Ziyarci Plateau

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnonin jihohin Arewa ta Tsakiya sun ziyarci jihar Plateau, kan hare-haren da miyagu suka kai.

Gwamnonin a yayin ziyarar ta'aziyyar sun bayar da gudunmawar N100m ga mutanen da hare-haren suka ritsa da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng