Yadda Dan Daba Ya Caka wa Limami Wuka Saboda Ya Hana Su Shan Wiwi a Kusa da Masallaci a Kano
- Yan sanda sun cika hannu da wani matashi a jihar Kano kan zarginsa da aikata kisan kai
- Matashin mai suna Yusuf Haruna wanda aka fi sanu da Lagwatsani ya caka wa wani limami wuka har lahira
- An rahoto cewa limamin ya hana su zukar tabar wiwi a kusa da masallaci ne wanda hakan ya fusata shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Jihar Kano - Jami'an rundunar yan sanda a jihar Kano, sun kama wani matashi mai suna Yusuf Haruna wanda aka fi sanu da Lagwatsani.
An kama Lagwatsani mai shekaru 18 a duniya kan zargin kashe wani limamin masallaci mai suna Sani Mohammed Shuaibu.
Matashin ya caka wa limamin wuka ne saboda ya hana su shan wiwi a kusa da masallaci, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwarsa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar a ranar Laraba, ya ce matashin ya kashe malamin ne yana tsaka da alwala.
Kiyawa ya ce:
“A ranar 31 ga watan Disambar 2023 da misalin 7:30 na dare, an samu rahoto daga wani mai suna Musa Yunusa da ke unguwar Jakara Kano cewa wani Yusuf Haruna ya daba wa Malam Sani Mohammed Shuaibu wuka a baya yana tsaka da alwala da misalin karfe 7:00.
“Ya soke shi da wuka ne a kan ya yi masa gargadi da ya daina zukar tabar wiwi a kusa da masallaci."
Kwamishinan yan sandan Kano ya yi martani
Kwamishinan yan sandan jihar Kano, Mohammed Usaini Gumel, ya ba al'umma tabbaci kan kudirin rundunar tsaroin na gudanar da cikakken bincike a kan al'amarin.
CP Gumel ya mika godiyarsa ga jama'a kan irin dumbin goyon bayan da suke ba rundunar sannan ya bukace su da su kai rahoton faruwar laifuka ofishin yan sanda mafi kusa da su.
Har ila yau, kwamishinan ya jaddada muhimmancin hadin kai wajen tabbatar da doka da oda a jihar.
Daga karshe, ya sanar da cewa za a zurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu da zaran an kammala bincike.
An harbe wani limamin masallaci
A wani labarin kuma, mun ji cewa antoni Janar na New Jersey ya sanar da rasuwar limamin masallacin New Jersey da aka harba da bindiga a ranar Laraba, inda ya ce ba kisan bambancin addini ba ne.
An harbi Hassan Sharif a wurare daban-daban a jikinsa a harabar masallacin da ke Newark, yamma da New York, inda ya mutu jim kadan bayan kai shi asibiti.
Asali: Legit.ng