Binciken N37bn: Ana Barazanar Cafko Ministar Buhari a Kan Yi wa Hukumar EFCC Taurin Kai

Binciken N37bn: Ana Barazanar Cafko Ministar Buhari a Kan Yi wa Hukumar EFCC Taurin Kai

  • Sadiya Umar Farouq ta ki amsa goron gayyatar da hukumar EFCC ta kai mata domin amsa tambayoyi
  • EFCC mai yaki da rashin gaskiya ta bukaci tsohuwar ministar ta zo domin a ji dadin yin bincike a kan ta
  • Tun da ‘yar siyasar tayi watsi da gayyatar, watakila babu yadda EFCC za ta yi illa ta sa a cafko mata ita

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Sadiya Umar Farouq za ta iya jawowa kan ta matsala a sakamakon bijirewa gayyatar da hukumar EFCC tayi mata a jiya.

Punch ta rahoto cewa jami’an hukumar EFCC za su iya cafko Sadiya Umar Farouq saboda ta ki zuwa gabansu ta amsa tambayoyi.

Sadiya Umar Farouq
Ana neman Sadiya Umar Farouq a EFCC Hoto: @OfficialEFCC
Asali: Twitter

EFCC v Sadiya Umar Farouq

An bukaci tsohuwar Ministar jin-kai da cigaban al’ummar ta hallara ofishin hukumar yaki da rashin gaskiya a kan binciken da ake yi.

Kara karanta wannan

Alumundahar N37bn: Ministan gwamnatin Buhari Sadiya Farouq ta yi biris da gayyatar EFCC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

EFCC tana bincike a kan wasu N37.1bn da ake zargin sun yi kafa a lokacin da Sadiya Umar Farouq ta ke ofis a tsakanin 2019 da 2023.

Sadiya Umar Farouq ta karyata zargin

Rahotanni sun ce ana zargin an karkatar da kudin gwamnati a ma’aikatar jin-kai ta hannun wani ‘dan kwangila, James Okwete.

Tsohuwar ministar da take magana a shafinta na X, ta ce ba ta san wani James Okwete ba, ta nuna za ta dauki mataki a kai.

Wani jami’in bincike na EFCC shaidawa jaridar cewa har suka tashi daga aiki da kimanin karfe 6:00, tsohuwar ministar ba ta zo ba.

"Mun tashi aiki yanzu nan domin ba ta hallara a yau ba, kuma har karfe 6:00 tayi. Ta tabbata cewa ba za ta zo yau ba."

- Wani jami'in EFCC

Kara karanta wannan

Hukumar EFCC za ta yi wa Sadiya Farouk tambayoyi kan zargin karkatar da N37bn a gwamnatin Buhari

Ina Sadiya Umar Farouq ta shiga?

Wata majiya a hukumar ta ce watakila za a cafko Umar Farouq nan da mako guda idan ta gagara kawo kan ta gaban EFCC da kan ta.

Channels ta ce ‘yar siyasar ta shanya ma’aikatan EFCC na tsawon awanni ana sa ran za a gan ta a hedikwatar hukumar da ke birnin Abuja.

Idan zuwa gobe (yau), babu labarinta, majiyar ta ce za a iya bada umarni a kamo ta.

Kungiyoyi irinsu Accountability Lab Nigeria da makamantansu sun ce ya kamata EFCC ta nemi a cafke ‘yar siyasar domin ayi bincike.

Fetur bai tashi ba inji NNPC Ltd

Rahoto ya zo a jiya cewa kamfanin NNPC Ltd ya tabbatarwa ‘yan Najeriya babu shirin kara kudin man fetur zuwa N1, 200 halin da ake ciki

NNPC Ltd a wani jawabi ya yi kira ga ‘yan Najeriya su yi watsi da rade-radin tashin farashin man fetur kuma a san akwai isasshen mai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng