Bayin Allah Sama da 100 Sun Mutu Yayin da Bama-Bamai Suka Tashi a Wurin Taro Kusa da Masallaci

Bayin Allah Sama da 100 Sun Mutu Yayin da Bama-Bamai Suka Tashi a Wurin Taro Kusa da Masallaci

  • Bama-bamai sun fashe a jere a kusa da kabarin Janar Qasem Soleimani, wanda jirgin Amurka ya kashe a shekarun baya
  • Rahoto ya nuna cewa bama-baman sun halaka akalla rayukan mutane 103 yayin da wasu ɗaruruwa ke kwance rai hannun Allah
  • An samu wannan fashewa ne a tsakiyar mutanen da suka yi cincirindo suna bikin tunawa da tsohon sojan a Kerman

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Rahotanni daga ƙasar Iran sun nuna cewa aƙalla mutane 103 ne suka mutu sakamakon tashin bama-bamai biyu a jere ranar Laraba, 3 ga watan Janairu, 2023.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta tattaro, kafafen watsa labarai a kasar Iran sun ce bama-baman sun tashi ne a tsakiyar masu bikin tunawa da kisan Janar Qasem Soleimani.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kai hari a wani babban kanti a jihar Nasarawa, sun kashe mutum 4

Bama bamai sun tashi a Iran.
Bam Ya Halaka Rayuka Sama da 100 a Wurin Jana'izar Marigayi Janar a Iran Hoto: CNN
Asali: Facebook

Tashin bama-baman, wanda gidan talabijin na kasar ya kira "harin ta'addanci", ya zo ne a daidai lokacin da ake fuskantar tashin hankali a Gabas ta Tsakiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan lamari ya auku ne kwana daya bayan kashe mai lamba ta biyu a ƙungiyar Hamas, Saleh al-Aruri, wanda ya kasance abokin kawancen Iran.

An kashe mataimakin shugaban Hamas ne a wani hari da jiragen yaki mara matuki suka kai a yankin kudancin Beirut wanda jami'an Lebanon suka dora alhakinsa kan Isra'ila.

A ina bama-baman suka fashe?

Fashewar bama-baman ta faru ne a maƙabartar da aka binne Soleimani da ke kusa da masallacin Saheb al-Zaman a Kerman, cewar rahoton CNN.

Dubbannin magoya bayansa ne suka yi cincirindo a ƙabarin marigayin domin bikin tunawa da kisan da jirgin sojin Amurka ya yi masa karo na huɗu kenan.

Kara karanta wannan

Kano: Babban Malami ya faɗi mafita 1 tak da ta rage wa Gwamna Abba gabanin hukuncin Kotun Koli

Mataimakin gwamnan na Kerman, Rahman Jalali, ya ce fashe-fashen "harin ta'addanci ne." har yanzun babu ƙungiyar da ta ɗauki alhakin kai harin.

Adadin mutanen da fashewar ta shafa

Kamfanin dillancin labaran IRNA, wanda a farko ya fitar da rahoton cewa mutane 73 ne suka mutu, ya ce:

"Adadin waɗanda suka mutu ya ƙaru zuwa 103 biyo bayan wasu da suka jikkata sakamakon fashe-fashen sun cika."

IRNA ta ƙara da cewa wasu mutane 141 sun samu raunuka iri daban-daban sakamakon tashin bama-baman, inda wasunsu ke cikin "matsanancin yanayi."

Kamfanin dillancin labaran Tasnim na Iran, ya nakalto majiyar da aka samu na cewa, "jakukkuna biyu dauke da bama-bamai ne suka tashi" a wurin.

Miyagu Sun Halaka Babban Limamin Masallacin Jumu'a

A wani rahoton na daban Wasu tsageru sun halaka babban limamin Masallacin Jumu'a da wani ɗan acaba a sabon harin da aka kai jihar Filato.

Shugaban ƙungiyar Fulani GAFDAN, Garba Abdullahi, ya ce tuni aka sanar da jami'an tsaro abin da ya faru don ɗaukar mataki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262