Gwamnonin Arewa Ta Tsakiya Sun Fadi Abu 1 da FG Za ta Yi Kan Hare-Haren Plateau
- Gwamnonin jihohin Arewa ta Tsakiya sun kai ziyarar ta'aziyya kan mutanen da suka rasa ransu a jihar Plateau
- Gwamnonnin sun yi kira da gwamnatin tarayya da ta gano tushen rikicin domin samar da dauwamammen zaman lafiya
- A yayin ziyarar gwamnonin sun kuma bayar da gudunmawar N100m mutanen da haren-haren suka ritsa da su
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Plateau - Ƙungiyar gwamnonin Arewa ta Tsakiya (NCGF) ta buƙaci gwamnatin tarayya ta gano tushen kashe-kashen da ake yi a jihar Plateau domin samun dawwamammen zaman lafiya.
Jaridar Daily Trust ta ce Shugaban ƙungiyar, Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa, ya yi wannan kiran a Jos, a ranar Talata lokacin da ya jagoranci takwarorinsa a ziyarar ta’aziyya ga gwamnan jihar Plateau, Caleb Mutfwang.
A hare-haren da aka kai a jajibirin Kirsimeti a wasu ƙauyuka 23 na ƙananan hukumomin Bokkos, Mangu, da Barkin Ladi, an salwantar da rayukan sama da mutum 150.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sule ya bayyana hare-haren a matsayin ta’addanci tsantsa, sannan ya buƙaci a samar da na’urori na zamani domin gano masu aikata laifuka tare da daƙile ayyukansu a yankin Arewa ta tsakiya.
Wane kira gwamnnonin suka yi?
Gwamnan na Nasarawa ya ƙara da cewa an dade ana kai hare-haren kuma ya dage cewa dole ne masu ruwa da tsaki daban-daban su gano tushen matsalar tare da samar da dawwamammiyar mafita a gare ta.
A cewarsa:
"Ranka ya dade, mun zo ne domin neman da ka jajirce wajen gano tushen wannan lamari domin ba za mu iya cigaba da rayuwa a haka ba."
Baya ga kokarin da ake yi a matakin jiha, shugaban gwamnonin na Arewa ta Tsakiya ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta gano tushen kashe-kashen da ake ta fama da shi.
Ya ce ta haka ne kawai za a iya samo bakin zaren warware rikicin da ya shafe sama da shekaru ashirin ana fama da shi.
A cewarsa:
“Mun ga irin wannan yanayi a Rwanda domin ba zan kira abin da ke faruwa a Plateau rikicin manoma da makiyaya ba, domin ba shi ba ne."
Jaridar The Nation ta kuma rahoto cewa a yayin ziyarar, gwamnonin sun ba waɗanda hare-haren suka ritsa da su gudunmawar N100m.
Shugaba Tinubu Ya Ɗau Zafi Kan Harin Plateau
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya yi Allah wadai da hare-haren da aka kai a jihar Plateau.
Shugaban ƙasar ya umarci jami'an tsaro da su gaggauta shiga cikin dajin domin zaƙulo miyagun da suka kai hare-haren.
Asali: Legit.ng