Gwamnan Arewa Ya Fadi Babban Burin Tinubu Kan Talakawan Najeriya, Ya Roki 'Yan Kasar Kan Hakuri
- Gwamnan jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya ya shawarci 'yan Najeriya su yi hakuri da mulkin Tinubu
- Inuwa ya ce Tinubu ya himmatu wurin tabbatar da tsame talakawan kasar a cikin kangin talauci a Najeriya
- Legit Hausa ta ji ta bakin wasu mazauna Gombe kan rabon tallafin na gwamnan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Gombe - Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya ya bayyana himmatuwar Shugaba Tinubu kan taimakon talakawan Najeriya.
Gwamnan ya ce Tinubu da gwamnonin kasar sun zaku don ganin sun fidda mutane a cikin kangin talauci a kasar.
Mene Gwamna ke cewa kan Tinubu?
Inuwa ya bayyana haka a jiya Talata 2 ga watan Janairu yayin ba da tallafin rage radadi karo na biyu, Tribune ta tattaro.
Ku kara wa Tinubu shekaru 3 kacal, Sanatan APC ya fadi gaskiya kan wahala a Najeriya, ya tura bukata
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce shugaban kasar zai daidaita tattalin arzikin Najeriya nan ba da jimawa ba wanda hakan zai rage yawan talauci a kasar.
Ya kara da cewa abin da Tinubu ya saka a gaba shi ne dawo da martabar matatun mai musamman na Port Harcourt wanda zai yi matukar taimakawa a fannin inganta harkokin mai.
Wace shawara gwamnan ya bai 'yan Najeriya?
Ya ce:
" Yau ce ranar da muka sake raba kayan tallafi ga marasa karfi a jihar baki daya don rage wa jama'a radadi.
"Kamar yadda kuka sani tun bayan cire tallafin mai muke samar da hanyoyin rage wa jama'a radadi don inganta rayuwar mutanenmu.
"Muna sa ran wannan rabon kayan zai shafi akalla mutane dubu 420 a fadin jihar, kuma zamu ci gaba da yi don inganta mutane."
Inuwa ya ce duk da tashin farashin kayayyaki a kasar bayan cire tallafi, tabbas za a ci moriyar hakan nan ba da jimawa ba, kamar yadda Leadership ta tattaro.
Legit Hausa ta ji ta bakin wasu mazauna Gombe kan rabin tallafin na gwamnan a karo na biyu.
Zainab Ja'afar Jekadafari ta ce gaskiya ita ta ji labari amma bata san yadda ake rabon ba duk da yawan jama'a da aka ce sun ci gajiyar abin.
Wani dan jam'iyyar APC mai suna Muhammad Sani ya ce:
"Tabbas Gwamna Inuwa ya na kokari, wannan shi ne karo na biyu da ya ke rabon kayan kuma hakan abin a yaba ne."
Ya yi fatan ci gaba da tallafawa marasa karfi har karshen wa'adin gwamnan ya kare.
Ku yi wa Tinubu uzuri, Orji ya roki 'yan Najeriya
A wani labarin, Sanata Orji Uzor Kalu ya bai wa 'yan Najeriya hakuri kan halin kunci da ake ciki a kasar.
Kalu ya ce sun san irin halin da ake ciki a kasar amma ya na bai wa 'yan kasar hakuri a kan haka.
Asali: Legit.ng