An Rasa Rayuka da Dama a Wani Kazamin Artabu Tsakanin Yan Banga da Yan Bindiga a Kaduna
- An yi fafatawa mai zafi tsakanin ƴan banga da ƴan bindiga a ƙaramar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna
- A yayin fafatawar ƴan banga 19 sun rasa rayukansu yayin da ƴan bindiga masu ɗumbin yawa suka sheƙa barzahu
- Fafatawar ta auku ne bayan miyagun ƴan bindigan sun kai farmaki kan mutanenn yankin suna tsaka da ayyuka a gonakinsu
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kaduna - An yi wani ƙazamin faɗa tsakanin ƴan banga da ƴan bindiga a dajin Katakaki dake ƙarƙashin gundumar Kakangi a ƙaramar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna.
Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa a yayin artabun dai ƴan banga 19 sun rasa ransu yayin da ƴan bindiga masu ɗumbin yawa suka sheƙa barzahu.
Lamarin wanda ya faru da misalin ƙarfe 4 na yammacin satin da ya wuce kimanin kwanaki 10 da suka wuce, yana ɗaya daga cikin zazzafan artabu tsakanin ƴan banga da ƴan bindiga a yankin na Birnin Gwari.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An halaka ƴan bindiga sama da 40
Ƴan bindiga sama da 40 ne aka ruwaito sun mutu a faɗan da ya barke tsakanin su da ƴan banga lokacin da ƴan bindigan suka far wa mutanen ƙauyen a gonakinsu.
Wani shugaban matasan yankin, Shehu Randagi, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce an gano gawarwakin ƴan bindigan 19 a cikin daji, yayin da sauran ƴan bindigan suka tafi da sauran gawarwakin domin kada a gane su.
A kalamansa:
"Zazzafan artabu ne wanda ƴan bangan mu mutum 19 suka rasa ransu yayin da wasu biyu ba a gansu ba. Mun kuma gano gawarwakin ƴan bindiga 19 a cikin dajin Katakaki.
"Mutanen ƙauyen Dogon Dawa Daji, wani ƙauye kusa da iyaka da jihar Neja sun gaya mana cewa sun ƙirga garwarwakin ƴan bindiga sama da 50 ana tafiya da su a kan babura bayan artabun."
Shehu Randagi ya jaddada cewa mazauna yankin ne suke kare kansu daga ƴan ta’adda, domin babu jami'an tsaro ko ɗaya a Kudancin Birnin Gwari.
Me hukumomi suka ce kan artabun?
Shima shugaban ƙungiyar cigaban masarautar Birnin Gwari (BEPU), Ishaq Kasai, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma ce bayanan da suka samu sun nuna cewa ƴan bindigan sun yi asarar rayuka da dama.
Kawo yanzu dai babu wani martani a hukumance daga jami’in hulɗ da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar, ASP Mansir Hassan, domin ba a samu wayarsa ba kuma bai dawo da amsar saƙon da aka tura masa ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.
Ƴan Bindiga Sun Sace Mata da Miji
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu miyagun ƴan bindiga sun sace mata da miji da wani ƙaramin yaro a jihar Neja.
Ƴan bindigan sun tafka wannan ta'asar ne a ƙauyen Gwaram wanda ke makwabtaka da babban birnin tarayya Abuja.
Asali: Legit.ng