Hukumar NAHCON Ta Dauki Sabon Mataki Bayan Wa'adin Biyan Kudin Aikin Hajjin 2024 Ya Kare
- Maniyyata masu niyyar zuwa aikin Hajjin shekarar 2024 sun samu ƙarin wa'adin lokacin biyan kuɗin aikin Hajjin bana
- Hukumar Alhazai ta ƙasa (NAHCON) ta sanar da ƙarin wa'adin zuwa ranar 31, ga watan Disamban 2024
- Hakan na zuwa ne bayan wa'adin farko na ranar 31, ga watan Disamban shekarar 2023 ya ƙare ba tare da kammala biyan kuɗin ba
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Hukumar alhazai ta ƙasa (NAHCON) ta ƙara wa'adin biyan kuɗin aikin Hajjin shekarar 2024.
A wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata, mataimakiyar daraktan harkokin jama’a ta NAHCON, Fatima Sanda Usara ta ce sabon wa’adin ya kasance ranar 31 ga watan Janairun 2024 maimakon ranar 31 ga watan Disamban 2023.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa tunda farko hukumar na cikin ruɗani kan ƙarancin biyan kuɗin da jama’a suka yi, kuma wataƙila ta ƙara wa’adin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai NAHCON ta dage cewa za ta yi aiki da yawan maniyyatan da suka biya kafin ranar 31 ga watan Disamba.
Sai dai a ƙarshe hukumar ta ja da baya, inda ta amince cewa ƙarin wa’adin ya kasance abu wanda babu makawa sai an yi.
Wani ɓangare na sanarwar na cewa:
"Ƙarin wa’adin ya zo ne a kan damuwar da malaman addini, hukumomin jindaɗin alhazai na jihohi, gwamnonin Jihohi da sauran masu ruwa da tsaki suka gabatar."
Meyasa NAHCON ta ƙara wa'adin?
Usara ta bayyana cewa amincewar da gwamnatin tarayya ta yi na tsawaita wa’adin ya ba da dama ga daidaikun mutane su samu damar zuwa aikin Hajjin.
A cewarta:
"Gagarumin buƙatar neman tsawaitawa daga al'ummomin addinai daban-daban na nuna muhimmancin tabbatar da ba ɗimbin muminai masu sha'awar shiga cikin aikin Hajji samun damar zuwa.
"Saboda haka, NAHCON tana da yaƙinin cewa kafin cikar wa’adin, tare da tallafin sauran hukumomi ƴan uwanta, hukumar za ta tantance jimillar kuɗin aikin Hajjin 2024."
Usara ta yi nuni da cewa, ƙarin wa’adin zai samar da wata dama ga sabbin masu rajista su samu su yi kafin ƙarshen watan Janairu, sannan waɗanda ba su gama biya ba su cikasa sauran kuɗaɗen.
NAHCON Ta Samu Matsala Kan Rashin Cike Kujeru
A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar jindaɗin Alhazai ta ƙasa (NAHCON) ta bayyana damuwarta kan rashin biyan kuɗin aikin Hajjin shekarar 2024.
Hakan na zuwa ne dai bayan dukkanin alamu sun nuna cewa kujeru dubu 97 da aka warewa hukumar, ba za a iya cika su ba.
Asali: Legit.ng